Gwamnatin Filato Ta Dauki Nauyin Alhazai Guda 200

0
328

Daga: Isah Ahmed, Jos.

GWAMNATIN Jihar Filato da Kananan hukumin Jihar guda 17, sun dauki nauyin biyan kujerun Alhazai guda dari biyu (200) da zasu je aikin hajjin bana. Sakataren hukumar Alhazai ta Jihar Filato, Batista Auwal Abdullahi ne, ya bayyana haka, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Jos.

Ya ce a bana kujerun Alhazai guda 824 ne aka warewa Jihar Filato.

Ya ce “Alhazan da suka biya kudaden su tun a shekara ta 2020 da shekara 2021, aka fara dauka, a kujerun da aka warewa Jihar Filato.”

Sakataren ya yi bayanin cewa an kammala shirya komai na aikin Hajjin ga Alhazan Jihar Filato.

” An yiwa Alhazai bita kan aikin hajji an raba masu jakankuna da riguna kuma an yi masu allura. Yanzu muna jira a kammala yi mana Visa ne. Idan aka kammala zamu sanar da hukumar Alhazai ta Najeriya a sanya mana ranar da zamu fara tashi”

Ya yi kira ga Alhazai su zama cikin shiri kuma su zamanto masu bin doka da oda a nan gida Najeriya da kasar Saudiya.

Leave a Reply