Hukumar NEDC Ta Bayar Da Tallafin Buhunan Kayan Abinci Kimanin Dubu 38,000 Ga ‘Yan Gudin Hijirar Borno

1
269

Daga, Sani Gazas Chinade, Maiduguri.

A RANAR Asabar din da ta gabata ne Hukumar Raya Arewa maso Gabas NEDC ta bayar da tallafin buhunan Masara, shinkafa, spaghetti da kuma kayan abinci kimanin buhuna dubu 38,000 ga ‘Yan gudun hijirar Borno da kuma tubabbun ‘yan Boko Haram kusan 66 da iyalansu da sauran wadanda rikicin ta’addanci ya shafa a Jihar.

Da yake mika kayan tallafin ga gwamnatin jihar Borno, Manajan Darakta/CEO, NEDC, Alhaji Mohammed Alkali ya bayyana cewa an bayar da wadannan kayayyakin ne a matsayin tallafi ga ayyukan sake tsugunar da ‘yan gudun hijirar da ake yi a jihar.

Alhaji Alkali ya kara da cewa a sannu a hankali zaman lafiya ya dawo a yankin arewa maso gabas da kuma kokarin gwamnatin jihar wajen sake tsugunar da ‘yan gudun hijirar da ‘yan tada kayar bayan suka raba, ya zama wajibi hukumar ta taimaka wa yankin arewa maso gabas wajen samar da shirin tsugunar da jama’a a wani bangare na sake gina yankuna da al’ummomin da ‘yan tada kayar bayan suka rusa a baya.

Ya kara da cewa, duk da cewa gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamitin hukumomin da za su tabbatar da dawowar ‘yan gudun hijira da tubabbun ‘yan tada kayar bayan, amma hukumar ta ga ya dace ta samar da agajin jin kai ga wadanda ke sansanonin da kuma sabbin al’ummomin da aka sake tsugunar da su.

“Mun ga ya zama dole a taimaka wa gwamnatin jihar wajen samar da wasu abubuwan jin dadin rayuwa ta fuskar abinci domin wadanda ke kusa musamman wadanda ke sansanonin da wadanda suka koma yankinsu ko kuma suka sake tsugunar da su a wani wuri kafin a taimaka musu yadda ya kamata, domin kokarin gwamnatin tarayya ya tabbata don kara karfafawa gwamnatin ta Borno a kokarin da ta ke yi na kula da ‘yan gudun Hijirar da kuma tubabbun’ yan kungiyar ta Boko Haram.

Shugaban na hukumar ta NEDC ya kuma bayyana cewa hukumar ta sayo kayan abincin ne daga wani kamfanin sarrafa abinci a kokarin farfado da masana’antu masu fama da rashin kula a yankin da hakan ke barazana ga durkushewar su dungurungum.

A jawabinta lokacin da take karbar kayayyakin a madadin gwamnatin jihar Borno, Darakta Janar ta Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Borno (SEMA), Hajiya Yabawa Kolo, ta gode wa hukumar ta NEDC bisa wannan tallafin, tare da bayar da tabbacin cewa tuni shirye-shirye sun yi nisa wajen sake tsugunar da wadannan ‘yan gudun hijirar tare da kokarin mayar da su ya zuwa gidajen kakanninsu na asali.

Hajiya Yabawa ta jaddada cewa gwamnatin jihar ta dukufa wajen ganin an dawo da dauwamammen zaman lafiya a jihar Borno da ma yankin baki daya.

A cewarta, kayayyakin da aka gabatar sun hada da buhuna 10,000 na shinkafa 25kg, buhunan masara 10,000, katan spaghetti 4,000, man girki galan 4,000, barguna 5,000 da katifun roba 5,000 da makamantan su.

1 COMMENT

Leave a Reply