Gwamnan Kaduna zai ba da ilimi kyauta ga ɗaliban Kuriga

0
26

Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya yi tayin ba da ilimi kyauta ga ɗaliban makarantar Kuriga da aka kuɓutar a ƙarƙashin gidauniyarsa.
Gwamnan ya kuma sha alwashin sake gina makarantun firamare dana sakandaren Kuriga tare da samawa al’ummar yankin kayayyakin more rayuwa.

A jawabinsa ga ɗaliban gabanin tashinsu zuwa Kuriga a ranar Alhamis, Gwamna Sani ya ba su tabbacin cewar al’amarin yin garkuwa da su ba zai shafin batun ilminsu ba, inda yace an tabbatar da ingantaccen tsaro ga al’ummar garin kuriga domin su ci gaba da rayuwa cikin walwala da aminci.

“Na umarci gidauniyar uba sani wacce ta shafe fiye da shekaru 16 tana ba da ilimi da lafiya kyauta, ta ci gaba da kula dasu.

“Na kuma ba da umarnin a gudanar da gyare-gyare a makarantu da garin Kuriga, domin a wurina Kuriga gari ne me son zaman lafiya a jihar Kaduna”.

Ya kuma sanar da gudunmowar Naira miliyan 10 ga iyalan Shed Mastan, Abubakar Isah da ya mutu a hannun masu garkuwa da mutane, sannan ya yi tayin ɗaukar nauyin karatun ‘ya’yansa har zuwa matakin jami’a.

KU KUMA KARANTA:An saki ɗaliban makarantan Kuriga da aka sace a jihar Kaduna

“Gwamnatin jihar Kaduna za ta ci gaba da tallafawa karatun ‘ya’yan Malam Abubakar. Kuma za mu tallafawa iyalansa da gudunmowar Naira miliyan 10 domin halin da suka tsinci kansu a ciki. Malam Abubakar ya rasu ne sakamakon wata jinya da yake fama da ita. Muna roƙon Allah ya gafarta masa.

Sai dai gwamnan ya ki yin ƙarin haske game da yadda aka bi wajen kuɓutar da ɗaliban, inda ya dage akan cewar bayanin ba shi da mahimmanci.

A cewarsa, abinda keda muhimmanci shi ne gwamnati ta yi nasarar dukkanin ɗaliban ba tare da illata ko guda daga cikinsu ba.

Leave a Reply