Gobara ta tashi a hukumar shari’ar jihar Kano

0
99

Gobara ta tashi a hukumar shari’a ta jihar Kano inda ta ƙone wani ɓangare kurmus.

Aminiya ta rawaito cewa duka ofisoshin da ke ɓangaren da gobarar ta tashi sun ƙone kurmus, kuma har kawo yanzu ba a san dalilin tashinta ba.

Tashi gobarar a ranar talata ya tsayar da ayyukan hukumar cak.

Wani Ganau da ke aiki a hukumar ya shaidawa Aminiya cewa suna zaune suka hango hayaki na tashi daga wani ɓangare na hukumar.

“Mun idar da sallah ke nan sai muka hango hayaki na tashi daga cikin hukumar.

“Kafin mu san abin yi har motar hukumar kashe gobara ta shigo harabar hukumar inda suka shiga aiki,” in ji shi.

Batulu Isah Waziri, muƙaddashiyar Darakta-Janar na hukumar ta bayyana cewa tana ofishinta aka sanar da ita tashin gobarar inda ta je ta ga yadda gobarar ta lahanta ofisoshin daraktocin Hukumar da wasu kayayyaki.

KU KUMA KARANTA: Gobara ta tashi a kasuwar Gamboru da ke Maiduguri

“Lokacin da na je wurin gobarar tana kan ci, na ga yadda ta lahanta ofisoshin daraktocinmu guda biyu da wasu ofisoshi na ma’aikatansu wanda kuma kayayyakin aikinsu da suka haɗa da tebura da kujeru da takardu duk sun ƙone kurmus,” in ji ta.

Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi ya ce da zarar hukumarsu ta kammala haɗa bayanai game da dalilin tashin gobarar da kuma girman asarar da ta yi za su sanar da manema labarai.

Leave a Reply