Gobara ta tashi a kasuwar Gamboru da ke Maiduguri

0
108

Babbar kasuwar Gamboru ta yi gobara bayan wata biyar da wata gobara ta laƙume ɓangaren kasuwar.

Gobara ta tashi da tsakar dare a babbar kasuwar Gamboru da ke Maiduguri a Jihar Borno.

A safiyar Lahadi gobarar ta tashi, wata biyar makamanciyarta ta cinye wani ɓangare na kasuwar.

Zuwa lokacin da wakilinmu ya turo mana rahoto, gobarar tana nan tana ci.

Wasu shaidu a kasuwar sun shaida wa wakilinmu cewa wutar ta fara ci ne da tsakar dare daga ɓangaren masu sayar da kayan miya.

Zuwa wannan lokaci dai ba a kai ga gano asalin abin da ya haddasa gobarar ba.

Amma an girke jami’an tsaro domin daƙile ayyukan ɓata-gari.

Leave a Reply