Gobara ta ƙone ofishin ‘yan sanda a Kano

0
98

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce gobara ta ƙone ofishin ‘yan sanda reshen ƙaramar hukumar Nasarawa.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Hussaini Gumel, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a Kano ranar Litinin cewa lamarin ya faru ne da safiyar ranar Litinin.

‘’Da misalin karfe 05.45 na safe ofishin ‘yan sanda ya kama da gobara ya ƙone wani ɓangare na ginin ofishin.

”Wannan ya faru duk da irin gaggawar ɗaukar matakai da Hukumar kashe gobara ta jihar ta ɗauka,” cewarsa.

Gumel ya ce ana ci gaba da bincike don gano musabbabin tashin gobarar.

KU KUMA KARANTA: Gobara ta halaka wani yaro ɗan shekara 4 a Kano

‘’An killace yankin don hana masu shiga kallo da ɓata-gari shiga wurin, makamai da alburusai da ke ofishin suna suna nan a killace.

“A yanzu haka jami’in ‘yan sandan na tantance wasu takardu da abin ya shafa,” inji Kwamishina.

Leave a Reply