Fiye da kashi 70 na waɗanda aka kashe a Najeriya a watan Yuni a Arewa suke

0
364

Daga Fatima GIMBA, Abuja

Binciken ya ce yunƙurin da gwamnati ta yi na hana satar mutane bai yi nasara ba a watan Yuni sa’o’i 2 da suka wuce.

Wata ƙididdiga game da sha’anin tsaro a Najeriya ta nuna cewa kashi 75.6 na mutanen da aka kashe sakamakon hare-hare a watan Yuni a arewacin ƙasar suke.

Sabuwar ƙididdiga, wadda kamfanin Beacon Consulting Limited da ke nazari kan harkokin tsaro ya fitar a wannan watan, ta bayyana cewa an kai hari 338 a fadin kasar a watan na Yuni lamarin da ya kai ga sace mutum 651.

Kazalika an kashe “mutum 765. Wannan lamari ya faru ne a ƙananan hukumomi 185 da ke jihohi 36 da Abuja, babban birnin kasar.”

Alkaluma kan lamarin sun bayyana cewa kashi 28.6 na kashe-kashen sun faru ne a Arewa maso Gabas ( an kashe mutum 219 ), kashi 23.5 a Arewa ta Tsakiya ( inda aka kashe mutum 180), kashi 23.5 a Arewa maso Yamma (mutum 180 sun mutu).

Kazalika kashi 10.5 na kashe-kashen ya faru ne a Kudu maso Yamma ( an kashe mutum 80), yankin Kudu maso Gabas na da kashi 9.2 (an kashe mutum 70) da kuma Kudu maso Kudu mai kashi 4.7 (an kashe mutum 36).

“Kashi 75.6 na mutanen da aka kashe a watan Yunin 2022 na zaune ne a arewacin Najeriya,” in ji kididdigar.

Ta ƙara da cewa bincike ya nuna cewa galibin mutanen sun mutu ne sakamakon hare-hare da ake kai wa a musamman yankunan karkara – inda aka kashe mutum 350 a watan na Yuni, yayin da musayar wuta tsakanin ‘yan bindiga da jami’an tsaro ta yi sanadin mutuwar mutum 183, sannan kwanton-bauna ya yi sanadin ajalin mutum 79.

Haka kuma bincike ya nuna cewa a watan na Yuni an fi kashe mutanen Borno inda aka kashe mutum163, sai mutum 90 da aka kashe Benue, an kashe mutum 82 a Kaduna, mutum 65 a Neja dsa kuma mutum 42 a Zamfara.

Jihar Ondo ce ke kan gaba a cikin jihohin Kudu maso Yamma da aka yi kisa inda aka kashe mutum 55, yayin da a Kudu maso Gabas an fi kashe mutane a Ebonyi inda mutum 28 suka mutu.

An fi sace mutane a Sokoto

A game da satar mutane kuwa, Jihar Sokoto ke kan gaba da mutum 107. Jihar Kaduna ke biye mata inda aka sace mutum 92, sai Jihar Katsina inda aka sace mutum 90.

Sauran su ne Neja inda aka sace mutum 60, an sace mutum 56 a Zamfara, yayin da aka sace mutum 56 a Abuja, da kuma mutum 47 a Borno.

Rahoton ya ce a watan na Yuni, kokarin gwamnati ya yi matukar rage lamuran rashin tsaro da kashe-kashe sai dai bai rage yawaitar sace-sacen jama’a ba idan aka kwatanta da watan Mayun 2022.

Leave a Reply