Labarin yana gefen ku!

EFCC ta gurfanar da tsohon ministan lantarki, Olu Agunloye

1

Hukumar Yaƙi da Masu yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC), ta gurfanar da tsohon ministan wutar lantarki da ƙarafa, Mista Olu Agunloye a gaban kotu.

EFCC ta gurfanar da tsohon ministan a gaban mai shari’a Donatus Okorowo na babbar kotun tarayya, bisa zarge-zargen zamba da almundahana.

Mista Agunloye wanda aka gurfanar a gaban kotu a wannan Larabar, bai amsa laifin da ake tuhumarsa da su ba.

Alkalin kotun ya bayar da umarnin ci gaba da tsare shi a gidan gyaran hali na Kuje, har zuwa lokacin da za a bayar da belinsa.

KU KUMA KARANTA: Ba Ministar Jin-ƙai ce kaɗai ta aikata almundahanar kuɗi ba – Atiku

Ana iya tuna cewa, a watan Disambar 2023 ne EFCC ta bayyana Agunloye a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo kan zargin almundahana.

A cikin sanarwar da EFCC ta wallafa a shafinta na X (Twitter), ta sanya hoton tsohon ministan tare da yin kira ga jama’a da su ba da bayanan da za su kai ga kama shi.

Gurfanar da shi na zuwa ne bayan gayyatar tsofaffin ministocin ma’aikatar jin-ƙai, Sadiya Umar Farouq da Betta Edu kan zargin almundahanar sama da biliyan 40.

Tuni dai EFCC ta gayyace su domin amsa tambayoyin kan zargin da ake musu.

Daga bisani kuma hukumar ta karbe fasfo ɗin su, domin hana su fita daga Najeriya har zuwa lokacin da za a kammala binciken.

Leave A Reply

Your email address will not be published.