EFCC Ta Cafke Akanta Janar Na Kasa, Ahmed Idris Bisa Zargin Badakala Naira Biliyan 80

0
286

Daga; Rabo Haladu.

Babban Akanta Janar na Nijeriya, Ahmed Idris ya fada tarkon hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) bisa zarginsa da sama da fadi da karkatar da dukiyar al’umma.

Masanna kan lamarin sun shaida cewar EFCC sun samu nasarar kama Ahmed Idris da yammacin ranar Litinin a Jiharsa Kano inda suka wuce da shi zuwa Abuja domin fuskantar tuhume-tuhume da amsa tambayoyi.

Majiyarmu ta shaida cewar EFCC ta jima tana gudanar da bincike kan wata badakala ta a kalla Naira biliyan 80 da ake zargin an karkatar da su da sunan bada kwangiloli na bogi.

Kamfanonin da ake zargi da karkatar da dukiyar al’ummar suna da alaka da iyalai da abokan shi Akanta Janar din, kamar yadda bincike ya nuna.

Jaridar Premium Times ta bayyana cewa, a lokacin da bincike ya zurfafa, an gayyaci Mista Idris domin amsa tambayoyi sau da dama amma ya ki amsa gayyatar.

Leave a Reply