Dokar Taƙaita Zirga-Zirga: Soja ya harbe yaro har lahira a Zariya 

0
93
Dokar Taƙaita Zirga-Zirga: Soja ya harbe yaro har lahira a Zariya 

Dokar Taƙaita Zirga-Zirga: Soja ya harbe yaro har lahira a Zariya

Daga Idris Umar, Zariya

Da yammacin ranar Talata ne aka gudanar da jana’izar Isma’il Muhammada mazaunin Samaru wanda sojoji suka harba a ƙofar gidansu dake Unguwar Samaru da ke ƙaramar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna.

Shugaban ƙaramar Hukumar Sabon Gari, Hon. Injiniya Muhammed Ibrahim Usman ya samu halartar jana’izar wanda aka gudanar a garin na Samaru.

DPO na Samaru Division da Kwamandan Sojoji na Barikin Basawa, da Limamai da sauran al’umma sun samu halartar jana’izar.

Idan ba ku manta ba, a wani mummunan al’amari da ya jefa al’umma garin cikin ruɗani, wani soja ne ya bindige yaron ɗan shekara 16 mai suna Isma’il Muhammad a ranar Talata 6 ga watan Agustan 2024.

Lamarin ya auku ne a ƙofar gidan su yaron da ke kan titin Sarkin Fawa, a garin na Samaru da ke ƙaramar hukumar Sabon garin Zariya.

Ganau sun shaida wa wakilinmu cewa; kisan ya faru ne da misalin ƙarfe 9:00 na safe a lokacin da sojan ke sintiri tare da abokan aikinsa a Unguwar ta Samaru.

KU KUMA KARANTA: Al’ummar Kudancin Kaduna sun sa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

Inda suka buɗe wuta na kan mai uwa-da-wabi a kan al’umma da nufin ganin sun shige gida sakamakon dokar hana zirga-zirga da gwamnatin jihar Kaduna ta saka, sai dai harbin na sojan nan take Isma’il ya rasa ransa.

Wasu gungun mutane, da suka nemi a sakaya sunansu sun shaida wa manema labarai cewa; Isma’il da abokansa na tsaka da wasa ne cikin lumana a ƙofar gidansu, sai suka ga sojoji sun nufo kansu.

“Sai yaran suka shiga cikin gida domin tsira da rayukansu, sai kwatsam sojan ya nufi ƙofar gidan da gangan, ya soma harbi babu ƙaƙƙautawa. Isma’il da ke tsaye bakin ƙofar gidansu sai ya koma cikin gida ya kulle ƙofa nan take harbin bindiga ya same shi ya rasa ransa”, in ji su.

Harin na sojoji ya haifar da fushi da hassalar al’umma, inda al’umma unguwar suka nemi da a yi musu adalci bisa kashe yaron.

Iyayen yaron da aka kashe, a lokacin da suke yiwa wakilinmu bayani sun ce, yaron ta baya tsokalar faɗa kuma bai je ko’ina ba a wannan rana face ƙofar gidansu amma sojan nan ya zo bakin ƙofar gidan nasu ya yi masa harbi 2 don haka Allah zai mashi sakayyar duniya da Lahira.

“Mun kai kukanmu ga Allah tare da bin lamarin kamar yadda doka ta tanada ƙarshe yace, za su zura ido su ga wani mataki hukuma za ta ɗauka akan lamarin.”

“Domin shugaban sojoji ya zo da DPO na wannan gari duk sun zo don haka za mu zura idanu muga abin da za su yi sun ce za su yi adalci muna fatan yin adalcin. In ji mahaifin yaron, Malam Muhammad.

A nasa jawabin bayan kammala sallar jana’izar yaron shugan sojoji wato GOC mai kula da jihar Kaduna da Kano da Neja da Jigawa Manjo Janar Saraso ya yi da suka gama mitin da dattijon anguwa sai ya fito gaban dubban matasa ya basu hakuri yace, zaiyi bincike tare da yin adalci a cikin wannan lamari da ya faru yace yana son a gano me ya haifar da wannan hatsarin don daukan matakin adalci.

Shugaban ya ƙara da cewa fitowar sojojinsa ba da nufin yin ɓarna bane sai don kare rayuka da duniyoyin al’ummar ƙasa baki ɗaya don kowa nada labarin wasu ɓata gari suna amfani da zanga-zanga suka ɓata dukiyar jama’a yace hakan bai kamataba.

Bisa haka yace lamarin bai mashi daɗi ba kuma da ikon Allah zai sa a fara bincike cikin lokaci.

Ƙarshe ya nuna jin daɗinsa bisa yadda aka saurareshi yayi rokon Allah ya jikan yaron kuma yaba iyayensa hakurin na faruwar lamarin.

Bincike ya tabbatar da cewa dukkanin kwamandojin barukokin dake kewaye da Zariya sun halacci wannan anguwa saboda yadda lamarin ya dau zafi.

Amma zuwa haɗa wannan rahoton sarakunan da masu anguwanni sun kwantar da hankalin jama’a tare da zura ido don yin adalci ga iyayen wannan yaron.

Leave a Reply