An kama sojan da ya harbe mai zanga-zanga a Zariya

0
108
An kama sojan da ya harbe mai zanga-zanga a Zariya

An kama sojan da ya harbe mai zanga-zanga a Zariya

Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta tsare wani jami’inta da ya harba bindiga don gargaɗi ga masu zanga-zanga a garin Zaria na jihar Kaduna, inda harsashin ya samu wani yaro tare da halaka shi.

A wata sanarwar da rundunar ta wallafa a shafinta na X ranar Laraba, ta bayyana cewar a ranar 6 ga Agusta Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya ta samu kiran neman agaji saboda wasu ɓata-gari sun taru a Samaru, suna ƙona tayoyi a kan hanya da jifan jamia’n tsaro da duwatsu.

Hakan ne ya sa rundunar ta tura jami’anta zuwa wajen da niyyar tarwatsa ɓata-garin da kuma tabbatar da an bi dokar hana fita da gwamnatin Jihar Kaduna ta saka.

Sanarwar ta ƙara da cewa bayan zuwan sojoji wajen, ɓata-garin suka yi yunƙurin kai musu hari, abin da ya sanya wani soja harba bindiga don gargaɗinsu, amma tsautsayi ya sanya harsashin ya faɗa kan wani yaro ɗan shekara 16 mai suna Ismail Mohammed wanda ya kuma rasu.

KU KUMA KARANTA: Dokar Taƙaita Zirga-Zirga: Soja ya harbe yaro har lahira a Zariya 

“Bayan bayyana matuƙar ɓacin rai game da lamarin, Shugaban Rundunar Sojin Ƙasa Laftanal Janar Taoreed Abiodun Lagbaja ya aike da babbar tawaga ƙarƙashin Babban Kwamandan Runduna ta 1 Manjo Janar Lander Saraso don yin ta’aziyya ga iyayen yaron da aka kashe,” in ji sanarwar.

In za ku tuna, Neptune Prime Hausa ta kawo muku rahoton  cewa, da yammacin talata ne aka gudanar da jana’izar Isma’il Muhammad mazaunin Samaru wanda sojoji suka harba a ƙofar gidansu dake Unguwar Samaru dake karamar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna.

Sanarwar ta kuma ce tuni aka tsare tare da fara binciken sojan da ya yi harbin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here