Al’ummar Kudancin Kaduna sun sa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

0
69
Al'ummar Kudancin Kaduna sun sa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

Al’ummar Kudancin Kaduna sun sa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

Daga Ali Sanni

A wani mataki na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, mutanan Goska da Dangoma da ke Ƙaramar Hukumar Jama’a ta Jihar Kaduna sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.

Sun rattaba hannun ne a garin Dangoma tare da bikin mika cibiyar sauraron koke-koke game da laifuffukan cin zarafin mata da kananan yara da saurarnsu wacce kungiyar Global Peace Development (GDP) ta gina tare da tallafi daga kungiyar International Alert.

Daraktan Gudanarwa na ƙungiyar GPD na ƙasa, Ebruke Onajite Esike, ya jaddada muhimmancin wannan shirin, inda yace suna gudanar da irin aikin ne a unguwanni biyar da ke ƙananan hukumomin Chikun da Jama’a waɗanda suka fuskanci matsalolin rikici da tashin hankula a baya.

KU KUMA KARANTA: Majalisar wakilai ta buƙaci gwamnatin Tinubu ta dakatar da yarjejeniyar Samoa

A shekarar da ta gabata, GPD tare da tallafi daga International Alert, sun taimaka wa mutane 3,396 ta hanyar shirye-shirye daban-daban da suka hada da wayar da kan al’umma da basu horo da tattaunawa da samar da tsarin zaman lafiya da sulhu.

Shirye-shiryen sun taimaka sosai wajen magance muhimman abubuwan da suka shafi cin zarafin jinsi da haifar da zaman lafiya mai dorewa.

Wani ɓangare mai muhimmanci da aka rattaba hannu a kai shi ne ƙirƙirar Kwamitin zaman lafiya da haɗin Gwiwa, wanda zai rika kula da ayyukan makiyaya, tabbatar da bin dokokin  da kuma karfafa zaman tare don samun fahimtar juna da kuma hana afkuwar rikice-rikice  nan gaba a yankunan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here