Dan Takarar Gwamnan APC Ya Shiryawa ‘Yan Jaridu Bude Baki A NUJ Kaduna

0
287

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

DAYA daga cikin yan takarar Kujerar Gwamnan Jihar Kaduna a karkashin Jam’iyyar APC, Dakta muhammad Abdulmalik Durunguwa ya shirya yan Jaridu bude baki na musamman domin nuna kulawarsa agaresu bisa kokarinsu, jajircewarsu, da sadaukarwar domin tabbata al’amura sun cikin nasara a Jihar da kasar baki daya.

Dan takarar wanda ya Jagoranci wata tawagar izuwa wajen taron bude bakin wanda ya gudana a sakatariyar Kungiyar NUJ dake Kaduna, ya samu halartar yan Jaridu da dama Musulmai da Kiristoci maza da mata inda aka ci aka sha, kana aka gabatar da jawabai na karin dankon zumunci da fahimtar Juna a tsakaninsu.

Da yake jawabi bayan kammala shan ruwan a wajen taron, dan takarar Kujerar Gwamnan ya bayyana cewa ya shirya wannan zaman na musamman ne domin karrama yan Jaridun bisa kokarin da suke da irin jajircewarsu akoyaushe, sannan da nuna kaunar shi a gare su a matsayin tsohon abokin huldarsu a sakatariyar Kungiyar ta Jihar.

Durunguwa, ya kara da cewa shi mutum ne wanda ya dade yana hulda da mutane da yanayin hulda da mutane wanda hakan ya bashi damar kai wannan ziyarar tare yin bude bakin a cibiyar Kungiyar domin neman goyon bayansu a bisa kudirinsa na tsayawa Takarar shugabancin Jihar a matsayin Gwamna.

Ya ce “ni dan Kaduna ne kuma haifaffen Kaduna kuma dan Kudancin Kaduna wanda yasan lungu da sako na Jihar don haka ba wani abun da wani zai fada mun dangane da ciki da wajen Jihar Kaduna don haka ina kalubalantar duk wani da zai yi yunkurin ganin bata mana kasa.”

“Na fi kowa sanin abinda da mutanen karkara ke so ko suka fi bukata don na sha mangoro a titi, nayi wanka a rafi, naje farauta a daji don haka mene ne ake so, hakazalika nasan abubuwan da mutanen birni ke so, don haka nasan meye fanka kuma nasan meye iska mai dadi a daji, toh ashe kuwa ba wani zai fada mun komai.

“Burina kawai shi ne na tabbatar da mutumin Jihar Kaduna ko a Birni ko a daji a matsayin mutumin karkara, kana iya kwana lafiya ka tashi lafiya, kaje gonarka, ka cire amfanin gonar, kaje Kasuwa ka sayar ka sayo abin da kake so, kana ka dawo gida ka zaune lafiya cikin kwanciyar hankali kaci abun ka yadda kake so ba tare da tashin hankalin ba, wannan shi ne Babban burina.”

Acewarsa, idan al’ummar Jihar zasu ba shi dama, zai yi amfani da sashen Noma wajen yin amfani ya Farfado da tattalin arzikin Kasar baki daya bama Jihar kadai ba kana daga arzikin da suke da shi a Jihar tun da Allah Ya albarkace su da arziki musamman a Kudancin Kaduna.

Da take jawabin maraba bisa ga Dan takarar bisa shirya wannan bude bakin da ya yi tare da su, Shugaban Kungiyar Yan Jaridu (NUJ) reshen Jihar Kaduna, Kwamared Asma’u Yawo Halilu, ta yaba wa Dan takarar bisa wannan dama da ya basu, kana ta gode mishi bisa kokarin ya nuna karamci gare su.

Hajiya Asma’u, ta kara da cewa kungiyar za ta cigaba da tsayawa kai da fada wajen ganin ta aiwatar da duk wani aikin daya dace ta fuskar kwarewa a tare da duk ma’aikatansu, wanda a halin yanzu tuni sun yi nisa wajen ganin sun hada kan duka yan Jaridun tare kawata aikin.

A Karshe, Shugabar kungiyar ta NUJ, ta jinjinawa Dan Takarar bisa nuna kaunar da ya yi musu kasancewar shi ne mutum na farko da ya fara zuwa ziyartarsu da kam shi, kana har da shirya musu wata kwarya-kwaryar zaman shan ruwan na bude bakin Azumi watan Ramadana.

Leave a Reply