Dan Rabaran Tawani Na Aikin Gina Wa Musulmai Rijiyar Burtsatse A Kudancin Kaduna

0
360

By; USMAN NASIDI, Kaduna.

A KOKARIN inganta zaman lafiya tsakanin juna a kudancin Kaduna, dan marigayi Rabaran Tawani kuma Injiniya a sana’a, Injiniya Dauda Tawani ya yi aikin hakar rijiyar burtsatse ta miliyoyin naira a wani babban masallaci da ke yankin Fadan kamantan a karamar hukumar Zangon kataf dake Jihar Kaduna.

Da yake jawabi a wajen kaddamar da aikin hakar rijiyar a Fadan kamantan, Hakimin Fadan kamantan Mista Sama’ila Tawani ya ce aikin zai kara bunkasa soyayya da zaman lafiya a tsakanin Musulmi da Kirista a yankin.

Ya ce aikin wanda gidauniyar Tawani Family Foundation ta gudanar ya samu daukar nauyin aikin Injiniya Dauda Tawani, wani fitaccen dan yankin.

Hakimin ya kara da cewa aiwatar da hukuncin aikin hakar rijiyar burtsatsen, wani bangare ne na kokarin tunawa da marigayin mahaifinsu wanda ya rasu, kana tare da kara dankon zumunci tsakanin musulmi da kiristoci a yankin da ma Jihar baki daya.

A cewar Mista Sama’ila Tawani, rijiyar burtsatsen za ta rage matsalar karancin ruwa a masallacin a lokutan salloli biyar musamman a yanzu da al’ummar Musulmi ke gab da fara azumin watan Ramadan cikin kankanin lokaci.

Da yake yabawa wannan karamcin, babban limamin masallacin Imam Rilwanu Isiyaka Fadan kamantan, ya bayyana farin cikinsa da jin dadin aikin hakar rijiyar burtsatsen, inda ya kara da cewa, ayyukan na nuna soyayya da juna.

Imam Rilwanu Isiyaka ya ci gaba da cewa wannan wani aiki ne da wani wanda ba musulmi ba ya dauki nauyin yin aikin harkar rijiyar burtsatsen wacce ta kunshi miliyoyin naira ga wani babban masallaci karamar hukumar Zangon kataf kuma abu ne mai ban al’ajabi da albarkar Ubangiji.

Babban Limamin ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni da su yi koyi da irin nagartar Injiniya Dauda Tawani tare da inganta soyayya da zaman lafiya a kudancin Kaduna.

Shima da yake jawabi, Sarkin Hausawan Fadan kamantan Malam Ahmed Adamu Garba ya bayyana wannan al’amari na Allah a matsayin abin al’ajabi tare da addu’ar Allah ya sakawa mai bada agajin Injiniya Dauda Tawani da alheri.

Ya ce shekara da shekaru suna fuskantar matsalar karancin ruwa, amma Allah a cikin rahamar sa ya yi amfani da wanda ba musulmi ba wajen magance matsalar, sannan kuma ya yi addu’ar Allah ya kara musu zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin Musulmi da Kiristocin dake yankin.

Bugu da kari, sarkin ya yabawa wannan karamcin tare da kokarin masu bayar da tallafi, sannan ya kara da cewa tabbas hakan zai kara habaka soyayya da zaman lafiya a yankin.

A nasa jawabin, mai bayar da tallafin, Injiniya Dauda Tawani, ya ce ya yanke shawarar yin hakan ne na yin aikin hakar rijiyar burtsatsen ne a cikin masallacin bisa ga umarnin littafin addininsu mai wa’azin soyayya ga bil’adama.

Ya ce marigayi mahaifinsa wanda Rabaran ne a Cocin Baptist ya gaya musu cewa su so juna da inganta zaman lafiya a tsakanin bil’adama. Ya kara da cewa yana son zaman lafiya, kuma yana son zaman lafiya ya kasance a kodayaushe a cikin al’ummarsa da Jihar da ma kasa baki daya.

Injiniya Dauda Tawani ya ce hakan na daga cikin kokarinsa na mayar da al’umma baya, yayin da al’umma da dama da suka yi cunkoso domin nuna farin cikinsu suka bayyana ra’ayoyinsu, kana da shaida aikin yin hakar rijiyar burtsatsen.

Wasu daga cikinsu da suka zanta da manema labarai sun bayyana farin cikinsu, inda su ka ce hakan zai sa a samu zaman lafiya da soyayya da kwanciyar hankali a tsakaninsu. Sannan kuma sun yaba wa mai bada tallafi Injiniya Dauda Tawani tare da yin kira ga sauran attajirai da su yi koyi da wannan baiwar da Allah Ya yi masa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here