Connect with us

Gobara

Babban ofishin jakadancin ƙasar Kanada a Najeriya ya kama da wuta a Abuja

Published

on

Wani ɓangaren ginin ofishin jakadancin ƙasar Kanada a Najeriya ya kama da wuta rigi-rigi a babban birnin tarayya Abuja ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa wasu sassan ofishin jakadancin Kanada wanda ke a lamba 13010G Palm Close, Diplomatic Drive, Central Business District a Abuja ne suka kama ci da wuta.

Sai dai har yanzun babu cikakken bayani kan ainihin abin da ya haddasa tashin wannan gobara a babban ofishin jakadancin na ƙasar waje.

Amma hotunan da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna yadda hayaƙi ke fitowa daga ginin.

Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Gobara

abun fashewa a Yobe ya tashi a fitacciyar kasuwar dabbobi

Published

on

abun fashewa a Yobe ya tashi a fitacciyar kasuwar dabbobi

abun fashewa a Yobe ya tashi a fitacciyar kasuwar dabbobi

Wani abun fashewa da ake zargin bam ɗin da aka birne ne ya tarwatse a fitacciyar kasuwar dabbobin nan ta Buni Yadi dake ƙaramar hukumar Gujba ta jihar Yobe.

Wani mazaunin garin Buni Yadin, Ali Hassan ya shaidawa tashar talabijin ta Channels ta wayar tarho cewar, al’amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12 da rabi na ranar Juma’a, kuma ya raunata wata yarinya.

Shima kakakin shiya ta 2 na aikin wanzar da zaman lafiya na hadin gwiwa mai taken “Operation Hadin Kai”, Kyaftin Muhammad Shehu ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya ce sojoji sun yi nasarar gano wani bam din da aka birne a kasuwar tare da tarwatsa shi.

KU KUMA KARANTA:An kama ɓarayin da ke haurawa gidajen mutane suna sata a Yobe

Ya ƙara da cewa mutum guda da fashewar ta shafa, na samun kulawa a ɗaya daga cikin asibitocin da ke garin Buni Yadi.

Ya kuma jaddada cewa al’amarin ba harin ƙunar bakin wake bane illa kawai bam ne da aka birne a ƙasa.

Garin Buni Yadi mai tazarar kilomita 54 tsakaninsa da Damaturu babban birnin jihar, na cikin karamar hukuma a jihar da ta fi fama da ayyukan ta’addanci, inda ta kasance ƙarƙashin mayaƙan Boko Haram tsawon shekaru 2.

Continue Reading

Boko Haram

An tabbatar da mutuwar masu juna biyu a cikin harin da aka kai a Borno

Published

on

An tabbatar da mutuwar masu juna biyu a cikin harin da aka kai a Borno

An tabbatar da mutuwar masu juna biyu a cikin harin da aka kai a Borno

An kasha aƙalla mutane 18, yayin da wasu 30 suka jikkata bayan wasu jerin hare-haren da ake zargin wasu mata ‘yan ƙunar baƙin wake ne suka kai a jihar Borno a jiya Asabar, in ji shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta yankin.

Borno dai na cikin shekaru 15 na hare-haren masu iƙirarin kishin Islama wanda ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane tare da raba wasu miliyoyi da humallan su.

Duk da cewa sojojin Najeriya sun rage ƙarfin mayaƙan, amma har yanzu suna kai munanan hare-hare kan fararen hula da kuma wuraren tsaro.

KU KUMA KARANTA:Gobara ta tashi a matatar man Ɗangote

Barkindo Saidu, shine babban Daraktan Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Borno, ya ce wasu da ake zargin ‘yan ƙunar baƙin wake ne suka kai hari daban-daban a wajen bikin aure da jana’iza da kuma asibiti, inda suka kashe mutane tare da jikkata wasu da dama a garin Gwoza.

Saidu ya ce an tabbatar da mutuwar mutum 18, adadin da ya haɗa da ƙananan yara da manya da ma mata masu juna biyu.

Sai dai babu wata ƙungiyar ko wani mutun da ya ɗauki alhakin kai wannan harin.

Boko Haram da ISWAP da ta ɓalle kanta, su ne ƙungiyoyin ‘yan bindiga da suka fi yawan gudanar da ayyukan su a jihar Borno, wani babban yanki na karkara mai girman gaske.

Continue Reading

Gobara

Tinubu ya jajantawa mutanen da gobarar kasuwar Karu ta shafa

Published

on

Tinubu ya jajantawa mutanen da gobarar kasuwar Karu ta shafa

Tinubu ya jajantawa mutanen da gobarar kasuwar Karu ta shafa

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya miƙa saƙon jajensa ga ‘yan kasuwar da shaguna da dukiyoyinsu suka ƙone a gobarar da ta tashi a kasuwar Karu a daren Alhamis.

Sanarwar da hadimin shugaban ƙasar akan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngilale ya fitar a ranar Juma’a ta ce, shugaban ƙasar ya yi takaicin samun labarin gobarar da ta shafi wani sashe na kasuwar.

Da yammacin ranar Alhamis, gobara ta laƙume wani yanki na kasuwar, inda ta lalata ɗimbim dukiya da sauran kayayyaki masu daraja.

KU KUMA KARANTA:Gobara ta tashi a matatar man Ɗangote

Sanarwar ta ƙara da cewar, shugaban ƙasa na miƙa saƙon jajensa ga ilahirin ‘yan kasuwar da wannan mummunan al’amari ya shafa, sannan yana ba su tabbacin samun tallafi daga gwamnatinsa.

Shugaban ƙasar ya kuma yi ƙira da a riƙa taka tsantsan da ɗaukar matakan kariya, domin kare afkuwar gobara da sauran bala’o’i a nan gaba.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like