Ba Karamin Hubbasa Gwamnatin Yobe Ta Yi Na Kokarin Farfado Da Shirin Ilimi Ba – Hon. Zakariyau

0
348

Daga; Bashir Bello, Majalisa Abuja.

A SAKAMAKON ire-iren kalubalen daya ta’azzara wanda ya addabi bangarorin Arewacin Najeriya musamman ta fannin harkar tsaro, Gwamnatin Jihar Yobe ta yi yunkurin ganin cewa ta canza tsarin Ilimin Jihar da Kokarin ganin farfadowar sashen wanda ya samu nukusani a yankin.

Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Bade/Jakusko ta Jihar Yobe, Honarabul Zakariyau Galadima kuma shugaban kwamitin Dangantakar Tsakanin Majalisar a hirarsa da yan Jaridu, ya bayyana cewa abu ne wanda kowa ya sani irin kalubalen tsaro da aka samu a Jahohin Arewa na gabas amma yanzu Gwamnatin Jihar Yobe ta yi yunkurin tabbatar da samun nasara a fannin ilimin.

Ya kara da cewa abubuwan da aka lalata basu tsaya ga gine-gine ba har hanyoyi da gadoji, lamarin ya kai ga durkusar da harkokin Ilimi na wasu makarantu da dama a Jihar Borno da Yobe, amma cikin ikon Allah lokacin da suka samu shugaba mai duba al’amuran al’ummarsa, Allah Ya taimaka sun yi nasarar Farfado da harkar Ilimi a Jihar.

Ya ce “Allah Ya taimake mu an samu shugaba mai kishi wanda ya tsaya kai da fata don ganin halin da aka shiga na ta’adin yan ta adda da ya shafi harkar Ilimi, domin ba bu maganin wannan abun illa Jihar Yobe tasa a farfado da wannan sashen ta hanyar neman taimako a wajen al’ummar kasa baki daya wanda hakan yasa yan Jihar suka tara wani kudi daidai gwargwado tare da taimakon kananan hukumomi da masarautu.”

“Bayan wannan, aka zo aka bude asusun kasa baki daya don al’ummar kasa su taimaka, wanda Inshaa Allah za ayi matukar amfani da ita ta hanyar daya dace domin Gwamnan ya tsara wani Kwamiti wanda zasu gudanar da sarrafa wannan Kudi don a tabbatar da anyi amfani da Kudin ta hanyar daya dace.”

“Kuma za aye amfani da wannan Kudi ta fannin ilimi domin kula da duk abinda suka lalace a gyara. A Jihar Yobe muna da tsari domin idan ba a manta ba, tun lokacin Bukar Abba Ibrahim ya budi baki ya ce Bukar basa karewa a Jihar saboda idan wannan Bukar din ya sauka, wani Bukar din zai zo ya hau domin a kan wannan tsarin muke kuma wani abu ne mai karfi wanda ya kamata a yabawa Gwamnan.”

Honarabul Zakariyau, ya ci gaba da cewa basu da shakka ko kokwanto balle tsoro a kan yin hakan wanda idan wani yazo ya sauka daga teburinsa ko ya gama a kan inda yake, wani idan shi ma yazo anan zai ci gaba domin suna da yakinin a kan yin hakan domin wani al’amari ne wanda tun fil’azal sun saba da yin shi saboda ci gaban al’ummar Jihar.

Hakazalika, da yake tsokaci kan kudirin Majalisar Tarayya bisa gurbataccen man fetur da ake fama da shi a kasar, ya nuna jindadinsa game da yadda Majalisar ta tsaya kai da fata don ganin cewa an warware matsalar man da al’umma ke fuskanta domin ako yaushe aka samu akasi na gudanarwa ta fannin kasuwanci, da ya shafi al’umma, ya kamata shugabanni su nuna jajircewar su akai a samu maslaha akan lamarin.

Acewarsa, duk wani abun daya shafi al’ummar Kasar wanda ko da ba kyauta zasu shashi ba da Kudin su ne zasu saya kamar man fetur din ko abinci ne, muddun aka samu akasi a cikin shi, toh alamu na nuna akwai munafurci a ciki, ko dagangar ko a rashin sani aka yi, toh ba za a sani ba har sai an bincika ansan mene ne, dalilin faruwar lamarin.

A karshe, ya shawarci Gwamnati da ta dauki matakin sakawa al’ummar Kasar daidai gwargwado bisa asarar da suka yi, kana da yaba wa irin wannan kudiri da manufofin Majalisar domin muddun idan ba su tsaya kan irin wannan al’amarun ba, alamun hakan na nuna gazawarsu.

Leave a Reply