Makon Wasanni: SWAN Kaduna, Ta Karrama Kwamishinan Wasanni, Shugaban AYCF Da Sauran Su

0
352

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

A BISA Kokarin da suke na ganin an inganta sashen wasannin motsa jiki a Kasar Najeriya, Kungiyar Marubutan Wasanni ta Kasa (SWAN), reshen Jihar Kaduna ta gudanar da makon wasannin tare da karrama wasu al’umma da lambar yabo na girmamawa ciki har da Kwamishinan Wasanni na Jihar Kaduna Honarabul Idris Nyam da Shugaban Kungiyar Tuntuba Ta Matasan Arewa (AYCF) Kwamared Shettima Yarima.

Taron karramawar da bada lambar yabon wanda ya gudana a dakin taro na gidan Sardauna dake Jihar Kaduna a ranar Asabar din daya gabata, ya biyo bayan kammala shirin makon wasannin motsa jikin da aka gudanar tun daga ranar 20 ga watan Maris izuwa ranar 25 ga watan Maris ta shekarar 2022.

An shirya wadannan wasannin ne da zummar kara inganta sashen wasannin da kulla kyakkyawar alaka a tsakanin al’umma wadanda suka hada da yin wasanni tsakanin makarantu, ma’aikatun Kafafen Yada Labarai, kana da kokarin nuna bajintar da ke tsakanin kowace al’umma kamar yadda ma’aikatan Gidan Talabijin na DITV suka lashe gasar kwallon Kafa na Kafafen Yada Labarai.

Da yake jawabi a wajen taron, Honarabul Idris Nyam, ya bayyana farin cikinsa bisa irin Kokarin da Kungiyar ta ke yi na ganin cewa ta samar da kyakkyawar yanayi da fahimta a tsakanin al’ummar Jihar ta hanyar ware mako guda na shirya wasannin motsa jiki daban-daban.

Kwamishinan Wasannin, ya kara da cewa ko shakka babu ma’aikatar wasannin ta Jihar Kaduna karkashin Jagorancin shi a shirye ta ke domin ta marawa duk wata Kungiyar wasanni baya domin tabbatar da an samu duk wata nasarar da ake bukata, wanda hakan yasa karsashin hubbasan da Kungiyar Marubutan Wasanni ta (SWAN) ta ke yi yake matukar birge shi.

Ya ce “tun bayan dana kama aiki a karkashin wannan ma’aikata kuma na ci karo da Shugaban wannan Kungiyar ta (SWAN), na yi maka alkawarin za mu yi aiki tare kuma bayan hakan duk inda naje taro na kan ci karo da shi, wanda hakan ya sanya ya tabbatar mun da shi Jakadan ma’aikatar wasannin ta Jihar Kaduna amma a karkashin Kungiyar ta (SWAN).

A nashi jawabin, Shugaban Kungiyar Tuntuba Ta Matasan Arewa (AYCF), Kwamared Shettima Yarima, ya bayyana cewa wasannin motsa jiki wani abu ne wanda zai taimaka wajen inganta rayuwar al’umma musamman a mutane da shekarun suka dan ja baya bayan ga zaman ta wata hanya ta sada zumunta da kulla kyakkyawar mu’amala a tsakanin al’umma baki daya.

Acewar Shettima, wannan shi ne karo na farko da yake halartar wannan taron na Kungiyar (SWAN), amma ya yi alkawarin ci gaba halarta tare da tallafawa harkokin Kungiyar ta duk fuskar da ta dace, kana ya yaba da irin yunkurin da Kungiyar ta ke na ganin cewa ta hada kan al’umma baki daya musamman a Jihar ta Kaduna.

Hakazalika, wasu daga cikin manyan mutanen da aka karrama da lambar yabo na girmamawar a wajen taron a bisa irin kokarin da suke ba sashen wasannin, sun hada da Makarantar Kadwel, Alhaji Abdulfatai Aremu (Mayekun), Bishop Ademola Idowu Tinuoye, Honarabul Ibrahim Yusuf Zailani, Alhaji Shehu Aliyu ( Dan Malikin Kasar Hausa), da sauran wasu al’umma.

Leave a Reply