Connect with us

Labarai

Soyayyar shekaru tara ta ƙare a bala’i, yayin da budurwa ta ƙona saurayinta a gidansa, ta kuma kashe kanta

Published

on

Daga Fatima MONJA, Abuja

Labarin Masoyan biyu, Boluwatife Bamidele, da Ifeolowa, labarin soyayya ne ta yau da kullum wanda suke sa ran yin aure da tara zuri’ah.
Soyayyar shekaru tara ta ƙare a bala’i inda masoyan suka mutu gabaki ɗaya a dalilin cin amana.

Wadannan matasan masoyan sun yi baiko ranar 4 ha watan Oktoba 2021, dan tabbatar wa juna da duniya dagaske suke, kafin Boluwatife ya tafi ƙasar Kairo binkice kan kore makiyaya. Ya dawo ƙasar nan a farkon wannan wata dan yayi wa masoyiyar tashi Ifeolowa, bazatan kyauta ta zagayowar ranar haihuwarta. Dawowar da akayi domin farinciki tayi sanadin mutuwar Masoyan duka biyu.

A ranar Lahadi 17 ga watan Yuli ne Ifeolowa ta cilla wuta a gidansu dake Koka kusa da Osogbo, bayan ta gano masoyin nata na neman wata daban wanda har sun haihu da ita, bayan ita bata samu haihuwar ba.

Matashiyar buduwar ta gudu bayan aika-aikar da tayi, baa sameta ba sai ranar da aka kai ta Babban asibiti a dake Oshogbo a mace, inji lauyan ta.

Gabriel Adejare, daya kasance maƙoci ya ce “yaga Ifeolowa lokacin yana dawowa daga aiki tana tafiya ba takalma kuma cikin kayan ƙasan tufafi. Lokacin da yayi kusa da gidan su sai ya fara ganin hayaƙi, sai yayi kururuwa dan a kawo ɗauki ga Boluwatife, bayan Faith ƙanwar shi ta sanar musu yayanta cikin gidan.”

“Mun fasa tagogi 4 Kafin muka samu daman shiga mu fito da shi, muka kai shi asibiti, daganan aka tura mu asibitin koyarwa dake Ibadan, jihar Oyo.”

Bode ƙani, kuma lawyan Boluwatife ya sanar da folis da su nemo inda Ifeolowa take, domin be yadda da labarin kashe kanta da tayi ba. Yana ganin tayi hakan da gangan ne, don gudun tuhuma.

Amma kuma a safiyar jumma’a aka samu gawarta a ɗakin ajiye gawa tare da taimakon lauyanta.

Duk da Bode ya tabbatar da gawar ta Ifeolowa ce, babu wanda yasan sanadin mutuwarta.

An tabbatar da Ife ta canza muhalli zuwa Ilesa sannan ta kira lauyan yazo ya dauke ta a ranar jumma’ah.

Tasha guba ta ne kafin isowar lauyan nata, ta dai samu ta bashi wasu takaddu da ta rubuta kafin ta fita daga haiyacin ta.

Daga cikin abinda ta rubuta shine, “Abokai na na kwarai da suke sona kuma suke sauraro na Mummy Fife, DJ whizz, Mummy Laurel, Mhiz Ammie, Adeoluwafemi, Dimeji, Odunola, Tiara. Ina son ku duka na aiko muku wannan ne domin nuna godiya da soyayyar ku gareni.”

“Omobaba, VP, Alahusa Fourty, My baby, Mummy Love… ku tabbatar da tambarin Teembam ya ɗore, tare da nawa. Kada ku manta da IFETIFE.”

“Ban kashe abokin ku ba, dan dukan ku kunsan ina tsananin son shi, sannan na cigaba da son shi har yanzu da nake gaɓar mutuwa. Kuyi bincike da kyau, musamman Omobaba da Fourty. Na dogara daku, kuma nasan Boluwatife zaiji dadin hakan.

Ɗan sanda mai magana da yawun hukumar, ya tabbatar da mutuwar Boluwatife, ta sanadin wuta da budurwar sa ta cinna mai.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Sarkin Gwandu ya naɗa ɗan Buran ɗin Gwandu babba

Published

on

Sarkin Gwandu ya naɗa ɗan Buran ɗin Gwandu babba

Sarkin Gwandu ya naɗa ɗan Buran ɗin Gwandu babba

Daga Haruna Abdulrashid

Shugaban majalisar sarakuna ta jihar Kebbi, Mai martaba Sarkin Gwandu, Manjo-Janar Muhammadu Ilyasu Bashar Mni, ya karrama Shugaban hukumar jin daɗi da walwalar Alhazzai ta ƙasa, Malam Jalal Muhammad Arabi da sarautar (ƊAN BURAN GWANDU BABBA) inda mai martaba sarki ya aike da tawaga zuwa birnin tarayya Abuja domin gabatar da wannan karramawa zuwa ga Malam Jalal Arabi.

Da ya ke jawabi a madadin mai martaba sarkin Gwandu Alhaji Aminu Ahmad, Sarkin Fadan Gwandu ya bayyana cewa mai martaba sarkin Gwandu ya amince da bayar da wannan karramawa ga Malam Jalal ne a bisa jajircewa da kuma taimako da yake yiwa Alhazzan Najeriya tare da haɗin kai da yake bawa shugabanni a kan abin da ya shafi harkar aikin Hajji mussaman a bana.

Shi ma shugaban hukumar jin daɗin da walwalar Alhazai ta jihar Kebbi, Alhaji Faruƙu Musa Yaro Enabo, Jagaban Gwandu, ya bayyana jin daɗin shi matuƙa a kan wannan karramawar da aka yi wa maigidan shi.

Ya kuma yabawa mai martaba Sarkin Gwandu Manjo-Janar Muhammadu Ilyasu Bashar akan yadda yake gabatar da kyakkyawan jagoranci zuwa ga Al’ummar Gwandu.

Wannan bayar da takardar karramawa ta sarautar (ƊAN BURAN GWANDU) Sun haɗa da Alh Aminu Ahmed Sarkin Fadan Gwandu, Alh Aminu Abubakar Gulumbe Uban ƙasar Gulumbe, Alh. Mustapha Ka’oje Sarkin Bargun Ka’oje, Alh Lamiru Shehu Sakataren Sarakunan jihar Kebbi, Alh Faruƙu Musa Yaro Enabo Jagaban Gwandu, Alh Usman Osho da Alh Rilwanu Awwal.

Mai girma Shugaban hukumar Jin daɗi da walwalar Alhazzai ta jihar Kebbi, Malam Jalal Arabi, ya bayyana jin daɗin shi sosai ganin wanan karramawa da ya samu daga masarautar Gwandu.

Ya kuma ce jihar Kebbi ta zama gida a gareshi ganin yadda yake samun karramawa da mutuntawa a jihar ya kuma bayyana mana irin mutunci da zumunci dake tsakanin shi da shugaban hukumar Jin daɗi da walwalar Alhazzai ta jihar Kebbi.

Alh Faruku Musa Yaro Enabo Jagaban Gwandu ya kuma yi godiya da jinjina zuwa ga Maigirma Gwamnan jihar Kebbi His Excellency Comrd Dr. Nasir Idris Ƙauran Gwandu akan irin yadda yayi ɗawainiya ga Alhazzan jihar shi.

Continue Reading

Labarai

Mun gana da shugaba Tinubu mun isar masa saƙon al’umma – Shaikh Bala Lau

Published

on

Mun gana da shugaba Tinubu mun isar masa saƙon al'umma - Shaikh Bala Lau

Mun gana da shugaba Tinubu mun isar masa saƙon al’umma – Shaikh Bala Lau

Daga Idris Umar, Zariya

A ranar Alhamis tawagar malaman Najeriya ta gana da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu dangane da halin da ƙasa ta ke ciki kan batun zanga-zanga da wasu ke ƙiran a yi dalilin halin matsi da tsadar rayuwa.

Rahoton sun nuna cewa jim kaɗanne bayan kammala ganawar, shugaban ƙungiyar Izala na ƙasa, Shaikh Abdullahi Bala Lau ya shaidawa manema labarai cewa shugaban ƙasa ya karɓi koken da suka je masa da shi.

“Mun faɗa mar halin da al’umma suke ciki na tsadar rayuwa, taɓarɓarewar tsaro da wahalar rayuwa, ya kuma ce dan Allah a ja hankalin al’umma a ba su haƙuri nan gaba kaɗan za a ga sauyi da gyara kan ƙorafe-ƙorafen da ake yi”. In ji Bala Lau.

KU KUMA KARANTA: Zanga-zanga ba gudu ba ja da baya – ‘Yan Najeriya

Daga nan kuma, Shaikh ɗin ya ja hankalin al’umma da su yi haƙuri su cigaba da addu’a, “ba mu da ƙasar da ta fi Najeriya kar mu rusa ƙasarmu da kanmu”. Inji Shaikh Bala Lau.

Continue Reading

Ilimi

Gwamnatin Katsina ta jaddada manufarta na ci gaba da bayar da horo ga malaman makaranta

Published

on

Gwamnatin Katsina ta jaddada manufarta na ci gaba da bayar da horo ga malaman makaranta

Gwamnatin Katsina ta jaddada manufarta na ci gaba da bayar da horo ga malaman makaranta

Daga Idris Umar, Zariya

Kwamishinar kula da ilimin firamare da na Sakandire ne ta bayyana ƙudirin gwamnatin jihar mai ci yanzu na ci gaba da bayar da ƙarin horo ga malamai a faɗin jihar don samar da ƙwararrun malamai da suka iya sarrafa na’ura mai ƙwaƙwalwa da za su yi gogayya da takwarorinsu a faɗin duniya.

Hajiya Zainab Musa Musawa ta bayar da tabbacin hakan ne a lokacin da ta kai ziyarar duba yadda shirin horar da malamai 10,000 da suka haɗa da sabbin ɗauka 7,000 a kan dabarun koyarwa na ƙarni na 20 ke gudana.

Kwamishinar ta kai ziyarar ne a makarantar firamare ta Modoji inda ake gudanar da bayar da horon na yini 3 wanda Ma’aikatar kula da ilimin firamare da na Sakandire, hukumar ilimin bai ɗaya da kuma haɗin gwiwa da shirin bunƙasa ilimi matakin jiha (TESS) suka shirya.

KU KUMA KARANTA: Da ilimi ake samun kowace irin nasara a rayuwa – Dauda Lawal 

Hajiya Zainab Musa Musawa wanda ta zagaya azuzuwa ta kuma tattauna da masu bayar da horon da Kuma malaman, ta bukace su da suyi amfani da lokacin su fahimci Abunda aka koyamasu don bunkasa tsarin koyo da koyarwa a jihar.

A yayin ziyarar dai Kwamishinar ta samu rakiyar Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Hajiya Mairo Mohamed Othman, Mai baiwa Gwamna shawarma akan ilimi Nura Sale Katsayal sauran Daraktocin Ma’aikatar.

Bayanin hakan na ƙunshe a cikin wata sanarwa wadda jami’in hudda da jama’a na Ma’aikatar Malam Sani Ɗanjuma Suleiman ya Sanyama hannu a katsina.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like