An Zabi Zainab Ali Musa A Matsayin Jami’ar Hulda Da Jama’a Ta Kasa A Kungiyar NCWS

0
285

Daga; JABIRU A HASSAN, Kano.

A RANAR 31 ga watan Maris ta 2023 ne, kungiyar matan Najeriya watau ” National Council For Women Societies” (NCWS) ta gudanar da babban taron ta na kasa a babban birnin tarayya Abuja, inda Kuma aka yi zaben shugabanni da zasu jagoranci kungiyar na tsawon shekaru 5.

Sannan an gudanar da zabukan shugabannin cikin nasara tare da kara jaddada hadin kai da gudanar da aiki tare tsakanin Ya’yan kungiyar inda aka zabi Hajiya Lami Lau a matsayin Shugaban kungiyar ta kasa sai Geraldine Utuk a matsayin mataimakiyar shugaba ta daya da kuma Deborah Ishaya a matsayin ma’aji.

Haka Kuma an zabi Hajiya Zainab Ali Musa a matsayin Jami’ar Hulda da Jama’a ta daya domin ganin kungiyar tana a sahun gaba wajen isar da manufofin ta da kuma kyawawan aikace-aikacen ta a fadin kasa baki daya.

Da take nuna godiyar ta ga mambobin kungiyar, Hajiya Zainab Ali Musa ta jaddada cewa zata rubanya kokarin ta wajen ganin kungiyar ta NCWS ta ci gaba da kasancewa abar misali cikin sauran kungiyoyi da ake dasu a kasar nan, tare da yin godiya ga dukkanin wadanda suke da hannu wajen kammala taron kungiyar da Kuma gudanar da zabe cikin nasara.

Leave a Reply