Connect with us

Labari

An Yi Taron Tattaunawa Kan Zaman Lafiya A Kaduna

Published

on

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

A KOKARIN ganin an samu kyakkyawar dangantaka a tsakanin mabiya addinai daban-daban, an gudanar da taron tattaunawa na shugabannin addinai a Kaduna da ke tarayyar Najeriya.

Taron tattaunawar dai kungiyar “Action Aid” ce ta shirya shi tare da hadin Gwiwar “Global Peace Development, da tallafin asusun Global Community Engagement and Resilence ( GCERF).

Da yake bayani a wurin taron, Darakta Esike Eburuke wanda ya samu wakilcin kodineta na Kaduna na kungiyar kokarin samar da ci gaban zaman lafiya na Kaduna, Uwargida Chat Sunday ta ce matsalar tashin hankali tsakanin mabiya addinai daban-daban na kara kaimi a Najeriya.

Ta bayyana cewa matsalar da ake samu ta tsattsauran ra’ayi na kara kaimi a cikin al’umma daban-daban musamman ta fuskokin al’adu, tsarin zaman yau da kullum da addini.

Inda ta kara da cewa cibiyoyin addinai da kuma al’umma su na kara samun matsalar tashe-tashen hankula kwarai.

Ebruke, ta bayyana hakan ya haifar da matsalolin tashe-tashen hankali na gaggawa da yawa da suka hada da samun matsalolin cikin gida da matsalar tsugunnar da mutane sakamakon rikici. kana ta tabbatar da cewa wadannan kalubalen da ake samu sun haifar da tsarin kasancewar Najeriya a matsayin kasa daya dunkulalliya.

Da yake nasa jawabin Darakta Janar na kula da harkokin addinai na Jihar Kaduna wanda ya samu wakilcin mai rikon Darakta a harkokin addinin Kirista, Uwargida Gora Catherine Safiya, cewa ta yi samar da batun zaman lafiya na da matukar muhimmanci a kowa ce al’umma.

Saboda haka ya na da kyau ga daukacin jama’a su fahimci juna, domin haka ta hanyar samun tattaunawa ne mutane za su fahimci juna, saboda haka ne suke yin kira ga wadanda suka shirya wannan taron da su ci gaba da yin taro irin wannan a cikin al’umma ta yadda jama’a za su san muhimmancin zaman lafiya.

A nasa bangaren Kodinetan kungiyar Action Aid, Anicetus Atakpu cewa ya yi dalilin gudanar da wannan taron a Kaduna shi ne domin a samu karfafa dangantaka tsakanin dukkan bangarorin da nufin yin maganin matsalar samun tsattsauran ra’ayi tsakanin mabiya addinai da suka yi Imani.

Ya kuma yi bayanin cewa shugabannin addini na da muhimmiyar rawar da za su taka wajen dakile matsalar tsattsauran ra’ayi da kuma maganin samun yawan tashe tashen hankula.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai wakilin kungiyar Jama’atunnasrul Islam na Jihar Kaduna Alhaji Ibrahim Kufena, wakilan kungiyoyin Matasa daga bangaren addinin Kirista da Musulmai sai kuma Sakataren kungiyar Kiristoci ta CAN reshen Jihar Kaduna.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labari

EMAS69 • LINK ALTERNATIF SPORTBOOK SBOBET

Published

on

By

Emas69 adalah bandar taruhan sportbook sbobet terlengkap yang saat ini sangat dikenal seluruh masyarakat Indonesia dengan melalui link alternatif Emas69. Pada permainan taruhan sportbook, setiap pertandingan sepak bola yang dilangsungkan dapat dijadikan sebagai tempat bagi seluruh masyarakat Indonesia untuk melakukan taruhan dengan menggunakan uang asli. permainan taruhan bola online dapat dilakukan dengan bebas sesuai dengan pertandingan yang berlangsung dan juga team sepak bola yang disenangi untuk memperoleh kemenangan dan kepuasan dari setiap taruhan sportbook di situs Emas69.

Continue Reading

Labari

Albashi mafi ƙaranci: Da babu gara ba daɗi – TUC/NLC

Published

on

Albashi mafi ƙaranci: Da babu gara ba daɗi - TUC/NLC

Albashi mafi ƙaranci: Da babu gara ba daɗi – TUC/NLC

Shugabannin ƙwadagon sun bayyana matsayar gabanin gabatar da tayin ga majalisun ƙwadagon don gamsar da su amincewa da hakan ya fi a’ala.

Gamayyar ƙungiyar ƙwadagon Najeriya ta ce tayin Naira 70,000 da shugaba Tinubu ya yi a matsayin mafi ƙarancin albashi da babu ne gara ba daɗi.

Shugabannin ƙwadagon sun bayyana matsayar gabanin gabatar da tayin ga majalisun ƙwadagon don gamsar da su amincewa da hakan ya fi a’ala.

KU KUMA KARANTA:NLC ta ƙira taron gaggawa bayan gwamnati ta jingine batun ƙarin albashi

Wannan dai na nuna a karo na farko tun neman mafi ƙarancin albashi mafi yawa a Najeriya Naira 615,00 ya sauƙo Naira 477,000, shugabannin ƙwadagon sun maida wuƙa kube ta hanyar yin na’am da tayin da gwamnati ta yi.

Bayan kammala ganawa babban sakataren ƙungiyar ƙwadagon ta TUC Komared Nuhu Toro ya ce sun amshi tayin da gabatar da hakan gaban majalisun su “mun kai majalisar ƙolinmu, tayin da shugaban ƙasa ya bayar sun kuma lamunta da shi da fatan Allah ya sa albarka…ai Naira 70,000 ɗin nan da babu ne gara ba daɗi.

Tuni ma’aikata na sassa daban-daban suka fara maida martani da mafi sauƙin shi ne na nuna ba abun da suka iya don jagorori sun miƙa wuya.

Malamin makaranta Muhammad Bello Nawaila ya ce ba wani tasiri da mafi ƙarancin albashin zai yi in an duba ɗan karen tsadar rayuwa.

Ita ma ƙungiyar gamayyar ƙungiyoyin arewa CNG da ke marawa gwagwarmayar ma’aikatan baya ta ce matuƙar shugaba Tinubu bai yi garambawul ga lamuran walwalar ma’aikata da matasa ba, za a iya fuskantar ƙalubale “mu na gujewa guguwar juyin juya hali a Najeriya matuƙar gwamnati ba ta farka ta ɗauki matakan gaskiya na zahiri ba.”

Alamu na nuna batun neman ƙarin mafi ƙarancin albashi zai dakata zuwa wani lokaci don ‘yan ƙwadagon sun yaɗa gora sai komawa kan batun tsadar rayuwa.

Continue Reading

Kasashen Waje

Mun yi wa shugaba Biden bayani kan harbin da aka yi wa Trump – Pennsylvania

Published

on

Mun yi wa shugaba Biden bayani kan harbin da aka yi wa Trump - Pennsylvania

Mun yi wa shugaba Biden bayani kan harbin da aka yi wa Trump – Pennsylvania

Sakataren tsaron cikin gida na Amurka, Alejandro N. Mayorkas ya fitar da wata sanarwa game da harbin da aka yi a wurin yaƙin neman zaɓen tsohon Shugaban ƙasar Donald Trump a jihar Pennsylvania da safiyar yau.

A cikin sanarwar, Sakataren tsaron cikin gidan na Amurka Mayorkas ya bayyana cewa, “Ni da Daraktan ma’aikatar leƙen asiri Cheatle mun yi wa Shugaba Biden bayani game da harbin da aka yi yau a Pennsylvania. Ma’aikatar tsaron cikin gida (DHS) da Ma’aikatar Leƙen Asiri suna aiki tare da abokan aikinmu, masu kula da kiyaye doka don gudanar da bincike kan harbin.

KU KUMA KARANTA:Kotun Ƙolin Amurka za ta yanke hukunci kan takarar Donald Trump

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Muna Allah wadai da wannan tashin hankalin da kakkausar murya tare da yaba wa hukumar leƙen asiri bisa matakin gaggawar da ta ɗauka a yau. Muna tare da Shugaba Biden, tsohon Shugaba Trump, da yaƙin neman zaɓensu, kuma muna ɗaukar duk matakin da ya dace don tabbatar da tsaronsu. Kula da tsaron ’yan takarar Shugaban ƙasa da kuma taron yaƙin neman zaɓensu na ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da sashenmu ke ba da fifik

Tun farko Mai magana da yawun ma’aikatar leƙen asiri Anthony Guglielmi ya fitar da sanarwa a dandalin sada zumunta X, cewa, “Ma’aikatar leken asiri ta aiwatar da matakan kariya kuma tsohon Shugaban ƙasar yana cikin ƙoshin lafiya. Yanzu haka Hukumar tana gudanar da bincike, ta kuma sanar da Hukumar Binciken manyan laifuka ta FBI.”

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like