An tilasta wa mutumin da ya yiwa Tinkiya fyaɗe, ya ci mattacciyar ‘yar tinkiyar a Anambra

0
352

An tilastawa wani mutum mai matsagaicin shekaru, Onyedika Ezennaya sumba da cin ɗanyan naman wata matacciyar tunkiya a jihar Anambra, bayan da ya yi lalata da wata tunkiya.

Dangane da wani faifan bidiyo da ke tafe a kafafen sada zumunta, lamarin ya faru ne a ƙauyen Okpo da ke Ekwulobia, ƙaramar hukumar Aguata ta jihar. Bidiyon ya kuma nuna cewa mazauna ƙauye suna tilasta wa wanda ake zargin ya sumbaci matatciyar tunkiya a cikin dajin da ake zargin ya aikata laifin.

A bidiyon, anji muryar namiji yana bada labarin cewa, wanda ake zargin Mista Ezennaya, yayi jima’i da wata tunkiya a cikin daji, bayan da ya shaƙe ya karya rago (ɗaya daga cikin ‘ya’yan tinkiyar) kafin ya keɓe da uwar.

“Ya yi wa wata mahaifiyar tunkiya fyade, bayan haka, ya kashe rago, sannan ya karya ƙashinta, wannan mugun aiki na da abin tashin hankali ne da ƙyama!” muryar ta ce.

Mutanen ƙauyen, yayin da suke Allah wadai da wannan aika aika a matsayin haramtaccin abu a ƙasar, sannan kuma bidiyon ya nuna suna dukan wanda ake zargi yayin da suke tilasta masa ya ci ɗanyen naman tumakin daya kashe.

A lokacin da aka tuntuɓi jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a jihar, DSP Ikenga Tochukwu don jin ta bakinsa, ya shawarci jama’a da su kai wanda ake zargin zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa, domin shari’ar daji ba ta taɓa zama zaɓi mafi kyau ba, a duk lokacin da aka kama wanda ake zargi ko me lefi.

Leave a Reply