An Rantsar Da Sabon Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara

0
438

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

RAHOTANNIN da muke sanu daga Jihar Zamfara na cewa An rantsar da Sanata Hassan Muhammad Nasiha a matsayin Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara a jiya Laraba.

Alƙaliyar Alƙalai ta Jihar Zamfara, Kulu Aliyu ce ta rantsar da sanatan bayan ƴan majalisar dokokin jihar sun tsige Mahdi Aliyu Gusau daga muƙamin duk a yau Laraba bayan Kakakin Majalisar Dokokin jihar, Nasiru Mu’azu Magarya ya karanta wasiƙar da Gwamna Muhammad Bello Matawalle ya aikawa majalisar ta neman tantancewa da naɗa Sanata Nasiha a matsayin mataimakinsa.

Da wannan sauyin da aka samu a halin yanzu za a gudanar da zaben cike gurbi guda uku kenan a Jihar Zamfara da suka hada da na yan majalisun Jiha biyu da suka rigamu gidan gaskiya da kuma na Sanata Hassan Nasiha da ya zama mataimakin Gwamna.

Leave a Reply