An kashe gomman mutane a rikicin manoma da makiyaya a Chadi

1
117

Aƙalla mutum 23 aka kashe a yayin wata arangama da aka yi tsakanin manoma da makiyaya a kudancin Chadi, kamar yadda Ministan Watsa Labarai Abdraman Koulamallah ya bayyana.

Lamarin ya faru ne bayan kisan da aka yi wa wani Balaraben makiyayi inda aka yi rikicin tsakanin 17 zuwa 21 ga watan Maris a ƙauyuka uku da ke kudancin yankin Moyen-Chari, kamar yadda ministan ya bayyana a ranar Litinin.

Ƴan’uwa da abokan makiyayin da aka kashe waɗanda ke zaune a arewacin ƙasar da ke fama da rashin ruwa, sun jagoranci samame a ƙauyen wanda suke zargin a nan aka yi masa kwanton-ɓaunar da ya yi sanadin mutuwarsa.

Ministan ya tabbatar da cewa an samu zaman lafiya a wuraren da aka yi rikicin.

KU KUMA KARANTA: Rikicin ƙabilanci ya yi sanadin mutuwar mutum 42 a Chadi

Arangamar wadda aka shafe kwanaki bakwai ana yi kuma ta bazu zuwa ƙauyuka biyu, ta yi sanadin mutuwar mutum tara daga cikin Larabawa makiyaya, da kuma 14 daga mutanen Sara Kaba, daga ciki har da mata huɗu da yara biyu, kamar yadda Koulamallah ya bayyana.

Ya bayyana cewa an kama mutum 21 sakamakon wannan lamari kuma ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano waɗanda suke da hannu.

A gabashi da kudancin Chadi, wanda wuri ne da mutane da dama ke ɗauke da makamai, ana yawan samun arangama sakamakon manoma na yawan zargin makiyaya da barin dabbobinsu yin kiwo a cikin gonakinsu da suka yi shuka a ciki.

Akasarin irin wannan arangama kuma na faruwa ne a wuraren da ake samun kyakkyawan yabanya, da kuma yanayi mai kyau ga dabbobi masu kiwo.

Baya Chadi, irin waɗannan rikice-rikicen sun zama ruwan dare a Sudan da Sudan ta Kudu da Jamhuriyyar Tsakiyar Afirka da Kamaru da Nijeria wadanda wurare ne da ke da kyawun noma.

1 COMMENT

Leave a Reply