Fasto mai wa’azi da macizai ya tsallake rijiya da baya

0
72

Wani Fasto da mahaifinsa ya rasu cikin mintuna bakwai bayan maciji ya sare shi, shi kansa an garzaya da shi asibiti bayan maciji ya yi masa rauni.

Mutumin mai suna Cody Coots ya nemi mabiyansa da su kai shi wajen wani dutse inda Allah zai yi hukunci ko yana raye ko ya mutu.

Sai dai wani mabiyi ya kai shi asibiti, kuma likitoci sun ce macijin ya yi kusan yanke masa jijiyar jini ta wuya, wanda zai kashe shi.

Big Cody, wanda ya kai shi asibiti, ya ce: ‘Yawancin mutanen da macijin ya ciza a fuska sun mutu a cikin minti biyar zuwa 10.

Mahaifinsa Jamie Coots ya mutu yana da shekara 42 a lokacin da macijin ya sare shi a shekarar 2014 a wannan Cibiyar Bishara a cikin cocin mai sunan Yesu a Middlesboro, Kentuck.

Ikklisiyoyi masu sarrafa maciji sun fara bayyana a cikin tsaunin Appalachian sama da shekara 100 da suka wuce.

Mutuwar mahaifin Cody ya sa shi shiga aikin fasto yana da shekara 23.

Cody da mabiyansa sun yi imanin ci gaba da yin kasada ga lafiyarsu – da rayukansu – a wa’azinsu duk ranar Lahadi lokacin da masu ibada suka ɗora hannunsu a kan marasa lafiya.

Suna yin addu’a, rera waka da kuma sauraron wa’azin da Fasto Cody ya jagoranta, wanda yakan ɗauko macizai a cikin akwati ya ɗauki ɗaya ko biyu daga cikinsu a sama sa’ar da yake wa’azi.

Ya gaji yin wa’azi ga mabiyansa ne yana wasa da macizai.

Leave a Reply