An kama mutum 8 kan zargin kashe malami a Jami’ar Maiduguri

0
88

Rundunar ƴan sandan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ta ce ta kama mutum takwas da ake zargi da hannu a kisan wani malamin Jami’ar Maiduguri a ƙarshen makon jiya.

Mai magana da yawun rundunar, Daso Kenneth, ya shaida wa manema labarai cewa an kama mutanen ne bayan sun samu bayani daga shugaban jami’in tsaron Jami’ar.

Bayanai sun ce an kashe Dokta Kamal Abdulkadir, malami da ke koyarwa a Sashen Ilimin Motsa Jiki da Kula da Lafiya (Physical and Health Education), a ofishinsa.

Kakakin ƴan sandan ya ce shugaban jami’in tsaron jami’ar ya gabatar musu da ƙorafi cewa an ga wata gawa wadda daga bisani aka tabbatar ta Dokta Abdulkadir Kamal ce.

KU KUMA KARANTA: Sojojin Najeriya sun kashe ƴan ta’adda da yawa a Katsina da Zamfara

Ya ce nan-take suka aika jami’ansu wurin da lamarin ya faru inda suka ɗauki gawar zuwa asibiti domin yin bincike.

Daso Kenneth ya ce mutanen da suka kama sun soma taimaka musu wurin bincike a yayin da suke farautar ƙarin mutane da ake zargi da hannu a kisan malamin jami’ar.

Kawo yanzu ba a san musabbabin kisan malamin ba, sai dai wasu rahotanni sun ce an ga alamun raunuka sakamakon wuƙar da aka caccaka masa sannan aka sace motarsa.

Leave a Reply