Labarin yana gefen ku!

An haramtawa Jacob Zuma tsayawa takarar shugaban ƙasa a Afrika ta Kudu

4

Afrika ta Kudu za ta gudanar da babban zaɓen ta a ranar 29 ga watan Mayu mai zuwa, zaɓen da ake sa ran ya zama mafi fafatawa a yaƙin neman ƙuri’u tun bayan fara mulkin dimokuraɗiyya a ƙasar a shekarar 1994.
Ranar Alhamis, jami’an Hukumar Zaɓen Afrika ta Kudu suka tsame sunan tsohon shugaban ƙasar Jacob Zuma daga jerin waɗanda za su tsaya zaɓe a watan Mayu mai zuwa, abin da ya ƙara ɗumama yanayin siyasar ƙasar gabanin zaɓen.

KU KUMA KARANTA:Tarihin Rijiyar Bozundalla wadda ta yi shekaru sama dubu ba taɓa ƙafewa ba

Jam’iyyar ANC mai mulkin ƙasar na daf da yin asarar fiye kaso 50 cikin 100 na ƙuri’unta a karon farko tun bayan da ta hau kan karagar mulki a ƙarshen mulkin wariyar launin fatar ƙasar.

Jam’iyyar na ci gaba da asarar magoya baya sakamakon raunin tattalin arziƙi da zarge-zargen cin hanci da rashawa da rashin iya mulki.

A shekarar 2018 ne zarge-zargen cin hanci da rashawa suka hamɓarar da Jacob Zuma mai shekaru 81 daga kan karagar mulki, amma har yanzu yana da tasiri a siyasar ƙasar.

Zuma ya jima yana yiwa jam’iyyar MK me hamayya kamfe, tare da ƙiran ‘ya’yan tsohuwar jam’iyyarsa ta ANC da maciya amana a wani yunƙurin na komawa kan kujerarsa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.