An Bukaci Al’ummar Yarbawa Da Su Bayar Da Hadin Kai Da Goyon Baya Ga Bola Tinubu

1
363

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

SHUGABAN kungiyar al’ummar Yarbawa da ke Arewacin Najeriya da Abuja, Ambasada Mohammed Arigbabuwo, ya yi kira ga daukacin al’ummar Yarbawa da su tabbatar sun bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga tsohon Gwamnan Jihar Legas, Jagaban Bola Ahmed Tinubu domin cimma Burinsa na zama shugaban kasa a shekarar 2023 in Allah ya amince.

Wannan kiran na kunshe ne a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannunsa da aka rabawa manema labarai a ranar Juma’a inda ya ce kiran ya zama wajibi ga dukkan al’ummar Yarbawa abu ne mai matukar muhimmanci a kasa baki daya da kowa ya bayar da cikakken hadin kai da goyon bayansa ga wannan bawan Allah domin wadansu ma su yi koyi da abin da Yarbawan suka aikata. Ya kuma kara fadakar da al’umma baki daya da su ci gaba da yi masa addu’ar samun nasara a koda yaushe.

Ya ci gaba da cewa idan har wadansu suka fahimci irin hadin kai da goyon bayan da ake ba Bola Ahmed Tinubu zai taimaka masa wajen tsarewa tsara a tsakanin yan takara irinsa domin kowa ya game cewa ya samu karbuwa ga kowa.

Ambassado Arigbabuwo ya ce tarihin siyasar Jagaban, wata yar manuniya ce da ke nunin irin yadda ake aiwatar da aiki a samu nasara domin jin dadin daukacin al’umma baki daya, kuma hakan na bayar da wata alamar cewa ya na da kwarin Gwiwa, Marko da ingancin da zai iya gadon shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2023.

Ya bayyana Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin jagora abin koyi wajen rikon gaskiya da adalci wanda ke da tarihin kokarin bunkasa tattalin arzikinkasa da zai iya kai Najeriya tudun mun tsira.

Ya kuma yabawa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu bisa irin yadda yake bayar da muhimmanci ga masarautun gargajiya, sai ya shawarce shi da ya ci gaba da kai ziyara ga sarakuna “Obas,Obis da sarakuna” kamar yadda ya fara a kasashen Yarbawa.

Sai dai Ambasado Mohammed Arigbabuwo, ya bayyana bacin ransa bisa irin yadda wasu Yarbawa ke furta wasu kalaman da ba su da dadin ji game da tsohon Gwamnan wanda kowa ya Sani ba wani abu bane sai karya da neman yin yarfen siyasa kawai. Ya shawarci masu irin wannan halin da su gujewa aikata hakan su kuma sake tunani.

1 COMMENT

Leave a Reply