Al’ummar Garin Panbegua Sun Yabawa Gwamna El-Rufa’i Da FARMTRAC Bisa Aikin Hanya

0
315

Daga Rabo Haladu

AL’UMMAR Ganin Panbegua da na garin Kauru duk a cikin kananan hukumomin Kubau da Kauru dake jihar Kaduna sun dade suna fuskantar matsalar rashin hanya, wanda yanzu gwamnatin Jihar Kaduna Ta bada kwangilar ginawa domin suma amfana da romon mulkin damokuradiyya.

Hanyar Pambegua zuwa Garin Kauru hanya ce wadda shekara da shekaru al’ummar yankin musamman manoma suke neman gwamnatin Jihar tayi musu amma hakan yaci tura, hasalima hanyar wacce manoman yankin suke fuskantar matsalar jigilar amfanin gona.

Al’ummar sunce bisa ganin yadda gwamnatin Jihar Kaduna da Kamfanin FARMTRAC suka himmatu wajen aiwatar da aiki mai inganci, hakan yasa suke jinjiwa Kamfanin da Gwamnatin Jihar Na cewa yanzu suma zasu dare wajen cin gajiyar ayyukan Gwamnatin El-Rufa’i na raya kasa da al’umma.

Honarabul Shehu Yunusa Pambegua, shi ne dan majalisar dokokin Jihar Kaduna mai wakiltar mazabar Kubau, wanda kuma mazaunin garin Pambegua ne, ya bayyana cewa aikin hanyar yazo dai dai lokacin da Al’ummar suke bukantarsa wanda idan aka kammala ta al’ummar yankin wadanda mafi yawansu manoma ne zasu samu saukin jigilar amfanin gona da kuma bunkasa harkokin kasuwanci baki daya.

“ Matsayina na dan asalin wannan karamar hukumar naji dadi sosai da naga Kamfani na gida yana aiwatar da aiki mai inganci da nagarta, wani abin mamaki da jin dadi mutanan Garin sun tabbatar min da cewa baya ga aikin da Kamfanin yake yi shi Kansa mai Kamfanin yakan yi musu alheri idan ya Kawo ziyara. Gaskiya mun godewa gwamnatin Jihar Kaduna da Kamfanin FARMTRAC a kan wannan aikin hanyar wanda zai amfani dubban mutane bama yan yankin kadai ba” inji Shi

Daniel Duniya shi ne mataimakin shugaban kungiyar ‘yan Jarida ta kasa NUJ reshen Jihar kaduna, ya bayyana cewa babu abin da zasu cewa gwamnatin Jihar Kaduna sai godiya saboda sama da shekaru goma suna neman a yi musu hanyar amma hakan ya faskara.

Duniya wanda ma’aikaci ne a gidan Rediyon Jihar Kaduna (KSMC) ya yaba kokarin dan kwangilar na fara aikin babu kama hannun yaro, inda ya yi fatan gwamnatin Jihar za ta ci gaba da shimfudo wa mutanan karkara ayyukan raya yankunan su.

Alhaji Hussaini Dan Allahji, direba ne, a garin Panbegua ya bayyana cewa duk wani direban Mota mai zirga-zirga daga Panbegua zuwa garin Kauru har ya wuce kasuwar magani yasan yadda hanyar ta lalace duk kuwa da cewa ita ce hanyar da manoma suke amfani da ita wajen kai kayan abinci gida da kasuwanni.

Akan hakan ya bayyana jin dadinsu da matakin da gwamnatin Jihar Kaduna ta dauka na gina hanyar.

“Ya zama dole mu jinjinawa Dan kwangilar dake aikin hanyar bisa aiwatar da aiki mai inganci wanda bisa alamun da muke gani aikin zamu dade muna amfana dashi. Idan ka duba yadda suka fara aikin, gaskiya babu abin da zamuce sai godiya”

Shima a zantawarsa da wakilinmu ta wayar tarho shugaban Kamfanin na FARMTRAC Injiniya Sadiq Abubakar, ya ce Kamfanin su ya himmatu wajen ganin ya fito da martabar sunan kamfanonin cikin gida ta hanyar aiwatar da aiki mai inganci da nagarta inda yace Kamfanin sa zai tabbatar da cewa ya yi aikin da al’ummar Jihar kaduna zasu amfana na tsawon lokaci.

Injiniya Saddiq, haka zalika, ya dauki alwashin cewa duk wani aiki da gwamnatin Jihar kaduna zata bashi zaiyi shi mai inganci da nagarta kamar yadda Kamfanin ya yi na raya Garin Kachia da Kafanchan wajen shinfuda musu titi mai nagarta da sauran wurare a fadin Jihar kaduna baki daya.

Leave a Reply