Connect with us

Kannywood

Adam A Zango, jarumin mu na wannan makon

Published

on

Adam A Zango ɗan wasan kwaikwayo ne na Najeriya, mawaƙi, darakta, furodusa, marubucin, kuma ɗan agaji. An haife shi a watan Oktoba, 1985, a Zangon Kataf a jihar Kaduna. Kimanin dukiyarsa ta kai kimanin Naira miliyan 300.

Adam Zango, wanda aka fi sani da yariman Kannywood, na ɗaya daga cikin masu faɗa a ji a Kannywood. Ya samu karɓuwa gurin mutane dayawa, musamman mata saboda yanada kyau na halitta, da kuma iya wanka. Mutanen da suka sanshi da wanda ma basu sanshi ba sun sheda irin kyautar sa, da yadda baya qyashin raba dukiyar sa, a duk inda ya tsinci kansa. Ko a harkar wajen aiki da biyan ma’aikata, Adamu an sheda hannunsa a buɗe yake, baya ƙaramar harka.

Ya fara sana’ar sa tun a shekarar 2001 yana ɗan shekara 16. Ya fara da harkar waƙa ne, ya kuma kai matsayin fitaccen jarumin fina-finan Hausa a cikin ƙanƙanin lokaci saboda hazaƙarsa da ƙwazonsa.

Adam Zango yana da waƙoƙi da dama da suka yi fice kuma ya shahara a Najeriya da sauran ƙasashen waje. A shekarar 2014, ya samu lambar yabo ta gwarzon ɗan wasa a kyautar fina-finan Afirka. Ya kuma lashe kyautar gwarzon mawakin Kannywood na hip-hop, da kuma fitaccen jarumin Kannywood a kyautar fina-finan mutanen birni a shekarar 2015.

Adamu, a lokacin da yai bikin zagayowar ranar aurensa na shekara 3

Wasu daga cikin waƙoƙinsa sun haɗa da Soyayya, Aure, Gambara, da dai sauransu. Ya fito a fina-finai sama da 200, da suka haɗa da Basaja, Hindu, Bayan Rai, Shaheeda, da wasu silsila. Ya fito kuma a shirye-shiryen Farin Wata sha Kallo da Asin da Asin a YouTube.

Ganin cewa Kannywood na biyansa Average na 200k -500k a kowane fim, ya danganta da irin rawar da Adam Zango ya taka a fim ɗin, za a iya cewa wani muhimmin ɓangare na arziƙin Adam Zango ya fito ne daga fina-finan.

KU KUMA KARANTA: Saratu Zazzau ‘Dr Girema’ ta kwana Chasa’in ta amarce

Baya ga kasancewar Adam A Zango ɗaya daga cikin jaruman fina-finan da suka yi nasara, Adam A Zango yana ɗaya daga cikin manyan jaruman Kannywood da suka fi kowa kuɗi, tare da sauran jarumai kamar Ali Nuhu, Nazir Sarkin Waƙa, Rahama Sadau, da sauransu.

Kannywood

Kannywood ta ba wa Hisbah tabbacin goyon baya a Kano

Published

on

Bayan ce-ce-ku-ce, Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta sake zama da daraktoci da furdusoshi da jarumai da sauran masu ruwa da tsaki a Kannywood don tsaftace harkar fim da nufin kau da ayyukan baɗala a jihar.

A jawabansu daban-daban, Shugaban Ƙungiyar MOPPAN ta Ƙasa Dokta Ahmad Sarari da takwaransa na Jihar Kano Ado Ahmad Gidan Dabino da Shugaban Ƙungiyar Jarumai Alasan Kwalle sun nuna jin daɗinsu game da taron inda suka sha alwashin ba wa Hisbah goyon baya tare da alkawarin cewa nan gaba za a samu gyara a harkar fim ɗin.

Wannan shi ya kawo ƙarshen ce-ce ku-cen da aka yi ta yi game da ganawar Hukumar da ’yan fim na farko, wanda mafi yawansu suka ƙaurace wa bisa hujjar cewa Hisbar ba ta bi hanyar da ta dace wajen gayyatar su ba.

KU KUMA KARANTA: ’Yan Kannywood da dama sun ƙaurace wa taron da Hisbah ta gayyata a Kano

Hukumar ta sake miƙa musu goron gayyata a karo na biyu wanda suka amsa a ƙarƙashin jagorancin ɗan gidansu wato Shugaban Hukumar Tace Finafinai da Dab’i ta Jihar Kano Abba Almustapha.

Kwamanda-Janar na Hukumar Hisbah Shaikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa ƙorafe-ƙorafe da suke yawan samu daga Kanawa da sauran sassan Najeriya kan yadda ’yan fim ke nuna abubuwan da suka saɓa wa addinin Musulunci da al’adun Hausawa a cikin finafinansu ya sa suka ga dacewar zama da masu ruwa da tsaki a harkar fim don laluɓo hanyoyin kawo gyara a cikin harkar.

“Ita Hukumar Hisbah an kafa ta ne don ta saita al’umma a kan koyarwar addinin tare da yi musu katanga daga aikata munanan ayyuka.

“Muna so a laluɓo hanyoyin da za a rage nuna abubuwa da suke na tir tare da ci gaba da nuna abubuwa da za su dabbaka addinin da kyawawan koyarwar al’adun Hausawa a harkar fim,” in ji Daurawa.

A nasa ɓangaren, Abba Almustapha ya bayyana cewa tuni ’yan fim din suka amince za su zama masu bin doka.

Abba Almustapha ya jaddada cewa nan ba da dadewa ba hukumomin biyu za su shirya taron ƙara wa juna sani da ’yayan Kannywood don ilimintar da su kan abin da ya shafi fim ta fuskar addinin Musulunci inda za a gayyato fitattun malaman Musulunci don tattauna tare da laluɓo hanyoyin da za a kai harkar fim ɗin ga tudun mun tsira.

Continue Reading

Kannywood

Ɗan wasan ƙwallon ƙafa Ahmed Musa, ya cika alƙawari, ya sayawa Karkuzu gida

Published

on

Kamar yadda Neptune Hausa ta kawo labarin cewa shahararren ɗan wasan Nijeriya Ahmed Musa MON ya yi alƙawarin sayawa Baba Karkuzu gida a yau Talata, alƙawari ya cika.
Alhamdulillah an sayi gida an kuma karɓi takardun gidan.

Kamar yadda kuke gani a hoto Baba Karkuzu ne riƙe da Jessy ɗin Ahmad Musa tare da takardan gidan shi cikin farin ciki da godiyar Allah (T).

Jarumin Kannywood, Karkuzu ya makance, yana kukan neman taimako

Ga waɗanda suka taimaka, Baba yace a isar masa da godiya a gare su, Ubangiji Allah ya sakawa kowa da alkhairi, Allah ya biyawa kowa buƙatar shi, wanda suka taimaka kuɗi da wanda suka taimaka da addu’a.

Dukkan mu Allah ya sakawa kowa da gidan Aljannah, Allah ya dube mu lokacin da muke cikin tsanani, Allah ya suturta mu da suturar shi mara yankewa, Allah ya rufa mana asirin mu. Ameen ya Allah.

Continue Reading

Kannywood

Jarumin Kannywood, Karkuzu ya makance, yana kukan neman taimako

Published

on

Fitaccen jarumin Kannywood, Abdullahi Shuaibu wanda aka fi sani da Karkuzu ya makance kuma yana fama da rashin lafiya.

Jarumin, wanda aka yaɗa bidiyonsa a shafukan sada zumunta, ya nemi taimakon kuɗi, inda ya bayyana cewa ya yi rashin lafiya tun watan Disambar 2020.

Shuaibu ya fara fitowa a masana’antar nishaɗantarwa ta Hausa a shekarun 1980 tare da shahararriyar wasan kwaikwayo mai suna Karkuzu na Bodara wanda ya sanya ake masa laƙabi da Karkuzu.

A zantawarsa da wannan jarida bayan faifan bidiyo, Karkuzu ya ce, “Yanzu na makance kamar yadda nake magana da ku. Ina matuƙar buƙatar taimakon kuɗi. Ba ni da abincin da zan ci da ciyar da iyalina.

KU KUMA KARANTA: Yadda mutuwar Alhaji Mala na shirin ‘Daɗin Kowa’ ta jijjiga Kannywood

“Gidan da nake zaune yanzu za a sayar. Idan sun sayar da wannan gidan, ban san inda zan dosa ba. Don haka ne nake neman taimako daga ‘yan Najeriya da su kawo min agaji.

A ƙalla ‘yan Najeriya su taimaka min sayan wannan gidan da nake zaune.”

Dangane da makanta, ya ce, “An min aiki sau biyu, amma a ƙarshe likitoci sun ce glaucoma ce, kuma ba zan sake gani ba. Na yarda da hakan a matsayin makoma ta. Amma ya kamata ‘yan Nijeriya su taimake ni. Kawo min gidan nan, da abinci.”

Masana’antar Kannywood na da ƙungiyoyi da dama, amma akwai zargin cewa ‘yan wasan kwaikwayo da dama ba sa kula da su idan ba su da lafiya kuma suna buƙatar taimako.

Zuwa haɗa wannan rahoto, ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Najeriya Ahmad Musa ya ba shi kyautar naira dubu ɗari biyar, sannan ya ce a nemo gida na naira miliyan biyar zai saya masa.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like