Saratu Zazzau ‘Dr Girema’ ta kwana Chasa’in ta amarce

1
375

A ranar Juma’a, 14 ga watan Oktoban 2022, aka gudanar da shagalin bikin Saratu Zazzau, Dr. Girema a cikin shirin Kwana Casa’in mai dogon Zango.

Saratu Zazzau

Saratu Zazzau, fitacciyar jarumar Kannywood wacce ta fito a fim din Kwana Casa’in mai dogon zango a Dr. Girema ta yi aurenta jiya, ranar Juma’a, 14 ga watan Octoban 2022.

Jarumar ta amarce da angonta, wanda su ka kwashe lokaci mai tsawo su na soyayya wanda sai yanzu Allah yayi za su yi aure.

Ki

Sanin kowa ne cewa jarumar ta dade tana fim, sai dai bata shahara sosai ba sai a wannan karon da ta dauki roll mai kyau a Kwana Casa’in inda tayi farin jini kwarai bayan bayyana a shugabar wata makaranta.

A kwanakin baya BBC ta zanta da ita inda ta shawarci matan da basu shiga fim ba da su dakata, kada su shiga, su je suyi karatunsu sannan suyi aure.

Ta kuma bayyana dalilin da ya sanya auren ‘yan fim ba ya karko, inda tace akwai mazan da ke kallonsu a talabijin amma kuma niyyarsu akansu ba mai kyau bace. Wannan ya sanya da zarar sun auresu, babu jimawa sai su sake su.

Auren da tayi ya bai wa kowa mamaki, sai dai wakilin Labarun Hausa ya samu nasarar samun rahotanni har da hotuna ta hannun Zainab Baba Ahmed, wacce itama ta halarci bikin inda tace abu ya yi armashi.

Muna mata fatan alkhairi tare da addu’ar Allah yasa mutu ka raba. Ameen.

A wata hira da Aminiya Daily Trust ta yi da ita, ta shawarci masu shirin fara fim akan kada su shiga, idan kuma ya zama dole to su samu jagora na gari wanda iyayensu zasu damka su a hannun shi.

Hirarta da trust

Ta sha tarin tambayoyi akan masana’antar Kannywood har ake cewa matan masana’antar basa zaman aure inda tace sakin aure ya zama ruwan dare a ko ina, kawai na Kannywood ne ya fito fili.

Kamar yadda tace, babu matar da take fatan a sake ta, musamman su ‘yan fim da ke auren masu kudi.

1 COMMENT

Leave a Reply