A mai da hankali a Noma don rage Talauci da Yunwa – Obasanjo

3
232

Tsohon shugaban ƙasa cif Olusegun Obasanjo, ya yi kira ga ‘yan ƙasa da su ƙara maida hankali kan harkar noma a wani yunƙuri na daƙile fatara da yunwa a ƙasar.

Tsohon shugaban ƙasar wanda ya samu wakilcin uwargidansa, Mrs Bola Obasanjo, ya bayyana hakan ne a yayin taron ƙaddamar da ƙungiyar Matan Afrika manoma ta Platform in Smart Climate Agriculture da aka gudanar a Abeokuta, jihar Ogun.

Ya ce, abu mafi muhimmanci da yafi kawo ci gaba a rayuwa shine abinci, kuma idan ana maganar abinci, ana maganar noma ne.

“Ya kamata ‘yan Najeriya su ɗauki aikin noma da darajarsa da muhimmanci a matsayin tabbatacciyar hanyar fita daga yunwa da fatara domin hakan zai ƙari al’ummar ƙasar daga rashin tsaro da kuma bunƙasa tattalin arzikin kasa.” inji Obasanjo.

3 COMMENTS

Leave a Reply