A bai wa ‘Yan babbar Kasuwar Jos  dama su sake gina Kasuwar-Hayatu Liman

0
260

Daga Isah Ahmed, Jos

Ganin irin mawuyacin halin da ‘yan kasuwar da suke gudanar da harkokin  kasuwanci, a babbar kasuwar Jos da ta kone a shekarun baya suke ciki, na rashin wuraren da zasu gudanar da harkokin kasuwancinsu, da  yadda gwamnati ta kasa sake gina wannan kasuwa. ‘Yan kasuwar sun bukaci gwamnatin jihar Filato, ta basu dama su sake gina wannan kasuwa. Shugaban ‘yan kasuwar Alhaji Hayatu Liman ne, ya bayyana haka, a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

 Ya ce ‘Yan kasuwar da suke kasuwanci a babbar kasuwar Jos, suna cikin wani mawuyacin hali. Domin  duk wanda ya kalli yadda ‘yan kasuwar suke cin kasuwa a gefan kasuwar, zai tausaya masu saboda mawuyacin halin da suke ciki.

 Ya ce ‘Yan kasuwar suna kasuwanci a rana, haka idan sanyi yazo suna cikin sanyi,  haka idan damina tazo suna cikin ruwan sama.  Hakan  ya faru ne  saboda kasa gyara wannan kasuwa, da ta kone.

 ‘’Mun yi zama da bangarorin gwamnati daban daban kan wannan al’amari, kamar Shugaban ma’aikatan gidan  gwamnatin Jihar Filato da Sakataren gwamnatin Jihar Filato, sauran masu fadi aji na gwamnatin Jihar Filato. Muka  basu shawarwari kan idan gwamnati, bata sami halin sake gina wannan kasuwa ba. A bamu dama mu ‘yan kasuwar da muke kasuwanci a wannan kasuwa, mu sake gina wannan kasuwa. In Allah ya yarda  cikin kankanin lokaci zamu sake gina wannan kasuwa.  Mu cigaba da harkokin kasuwancinmu,  harkokin kasuwanci ya sake dawowa a jihar Filato,  gwamnati ta sami hanyoyin  samun kudaden shiga’’.

 Alhaji Hayatu Liman ya bada tabbacin  cewa idan gwamnati ta basu dama, a cikin wata 6 in Allah ya yarda zasu sake, gina wannan kasuwa kamar yadda gwamnati take bukata da tsarin da take bukata.

 Ya ce gaskiya gwamnati ta sake gina wannan kasuwa a wannan lokaci,  ba karamin kudade za ta a kashe ba.

 ‘’Ko a lokacin da aka gina wannan kasuwa  lokacin da muke da karfin kudi a Najeriya, sai da aka yi shekaru 9, ana gina wannan kasuwa kafin a kammala. Domin an fara gina wannan kasuwa a shekara ta 1975, aka kaddamar da ita a shekara ta 1984. Kaga yanzu gwamnati ta ce za ta sake gina wannan kasuwa, a wannan hali na rashin kudi da ake fama da shi a Najeriya, ba mai yiwuwa bane’’.

Leave a Reply