NAFDAC ta haramta amfani da maganin tari na yara na kamfanin J&J

0
144

Hukumar NAFDAC da ke sanya idanu kan ingancin abinci da magunguna a Najeriya ta haramta amfani da maganin tari na yara na kamfanin Johnson & Johnson bayan ta gano cewa yana ɗauke da wani sinadari mai hatsarin gaske, kamar yadda ta bayyana ranar Laraba.

Gwaje-gwajen kimiyya da aka gudanar a kan maganin mai suna Benylin Paediatric sun nuna cewa yana ƙunshe da sinadarin diethylene glycol mai yawa, wanda ake zargi shi ya haddasa mutuwar ƙananan yara da dama a Gambia, Uzbekistan da Kamaru tun shekarar 2022.

Ana amfani da maganin don kawar da ciwon tari da kuma cutukan da ke da alaƙa da cushewar ciki, da zazzaɓi na yara ƴan shekara biyu zuwa 12, a cewar NAFDAC a saƙon da ta wallafa a shafinta na intanet.

“Gwaje-gwajen da aka gudanar a kan maganin sun nuna cewa yana ɗauke da sinadarin Diethylene glycol mai yawa kuma an gano shi ne yake haddasa cututtuka a bakin dabbobi,” in ji NAFDAC.

KU KUMA KARANTA: NAFDAC ta gano wuraren da ake madara, barasa da lemo na bogi

Idan ɗan’adam ya yi amfani da wannan magani zai iya fuskantar zafin mara da amai da gudawa da ciwon-kai da ciwon ƙoda da ka iya kaiwa ga mutuwa, a cewar hukumar ta NAFDAC.

Da aka tuntuɓi J&J kan lamarin, ya buƙaci a nemi ƙarin haske daga kamfanin Kenvue, wanda yanzu shi ne ya mallaki nau’in Benylin bayan ya saye shi a shekarar da ta gabata. Sai dai Kenvue bai ce komai ba kan wannan zagi ya zuwa wannan lokaci.

A watan Mayu na shekarar 2021 aka yi maganin da Najeriya ta haramta amfani da shi a Afirka ta Kudu inda ya kamata ya daina aiki a watan Afrilu na 2024. NAFDAC ta umarci mutanen da suka sayi maganin su kai shi ofishinta mafi kusa da su.

Leave a Reply