Labarin yana gefen ku!

An yi bikin ƙaramar sallah lafiya a Zariya

3

Daga Idris Umar, Zariya

Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ya samu halartar ƙaramar sallar (Idi-fitir) na bana lafiya.

Daga cikin manyan baƙin da suka samu marawa Sarkin baya sun haɗa da gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani sai ministan Environment Malam Balarabe Abbas da sauran manyan baƙi na nesa da na kusa.

Bayan kammala sallar Sanata Uba Sani ya nuna farin cikinsa da Allah ya kawo su wannan rana lafiya, kuma yayi ƙira da al’umma su ci gaba da addu’ar samun zaman lafiya ƙarshe ya yi fatan Allah ya maimaita mana.

Leave A Reply

Your email address will not be published.