Labarin yana gefen ku!

Biden ya yi alƙawarin kare Isra’ila daga harin ramuwar gayya na Iran

1

Shugaban Amurka Joe Biden ya yi alƙawarin bayar da “garkuwa mai ƙarfe” ga Isra’ila idan Iran ta kai mata harin ramuwar gayya bayan ta zarge ta da kai hari a ƙaramin ofishin jakadancinta da ke Damascus, babban birnin Syria har ma ta kashe janar biyu na rundunar sojojin Iran.

Biden ya sha wannan alwashi ne ranar Laraba duk kuwa da sukar da yake yi wa Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu game da kashe-kashe da yake yi wa Falasɗinawa da ke Gaza, musamman bayan kisan wasu ma’aikatan agaji bakwai kwanakin baya.

Iran tana “barazanar ƙaddamar da babban hari a Isra’ila,” Biden ya shaida wa manema labarai.

“Kamar yadda na gaya wa Firaiminista Netanyahu, za mu bai wa Isra’ila kariya mai ƙarfin gaske game da wannan barazana daga Iran da ƙawayenta,” in ji Biden.

KU KUMA KARANTA: Turkiyya ta dakatar da cinikayya da Isra’ila sai an tsagaita wuta a Gaza

“Bari na maimaita abin da na ce — za mu bayar da garkuwa mai ƙarfin gaske. Za mu komai domin kare tsarin Isra’ila,” a cewar Biden, wanda yake jawabi a tare da Firaiministan Japan Fumio Kishida.

Jami’an gwamnatin Amurka sun bayyana fargaba game da shirin Iran na kai wa Isra’ila harin ramuwar gayya bayan da a ranar 1 ga watan Afrilu dakarun Isra’ila suka kai hari a ƙaramin ofishin jakadancin Iran da ke Syria, inda suk kashe zaratan sojoji bakwai na rundunar ta musamman ta Revolutionary Guard ciki har da janar-janar biyu.

Shugaban Addinin Iran Ali Khamenei ya yi jawabi ga dandazon jama’ar da suka halarci sallar idi a Tehran, inda ya ce “gwamnatin shaiɗanu ta yi kuskure kuma dole a hukunta ta.”

“Harin da suka kai wa ofishin jakadancinmu, tamkar hari na a cikin ƙasarmu,” in ji shi.

Ministan Harkokin Wajen Isra’ila Katz ya yi wani kakkausan gargaɗi ga Iran a shafukan sada zumunta.

A wani saƙo da ya wallafa a shafin X, a harshen Hebrew da Persia wanda kai-tsaye ya tura wa Khamenei, Katz ya yi barazanar yin martani idan Iran ta kai hari a Isra’ila.

“Idan Iran ta kai hari a cikin ƙasarmu, Isra’ila za ta mayar da martani ta hanyar kai wa Iran hari,” in ji shi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.