Labarin yana gefen ku!

NAFDAC ta gano wuraren da ake madara, barasa da lemo na bogi

2

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Najeriya NAFDAC ta gano wasu rukunin shaguna sama da 240 da ake yin lemon kwalba na bogi.

Hukumar ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar bayan ta kai samame kasuwar Eziukwu da ke Aba a Jihar Abia.

A kasuwar, akwai jerin shaguna daban-daban waɗanda ke samar da lemon kwalba nau’i daban-daban ta hanyar satar fasaha da kuma amfani da sinadarai marasa inganci domin kwaikwayon lemon kamfanin na asali.

Hukumar NAFDAC ta bayyana cewa shagunan na yin jabun kayayyaki waɗanda suka haɗa da barasa nau’in Seaman Schnapps da Henessy da Four Cousins da Martell da sauransu.

KU KUMA KARANTA : Hukumar NAFDAC ta gargaɗi ‘yan Najeriya kan amfani da sabulun ‘Crusader’

Haka kuma shagunan suna sauya kwalba da gwangwani ga kayayyakin da suka lalace irin su Coca-Cola da madarar Peak da tumatirin kwalba na ketchup da sauransu.

Hukumar ta bayyana cewa samamen da ta kai ya yi sanadin lalata kwalayen jabun kayayyaki 1,500 waɗanda kuɗinsu ya kai kimanin miliyan 750 da kuma ɗaukar kwalaye 300 zuwa ɗakunan ajiyar NAFDAC.

NAFDAC ta bayyana cewa ta kama mutum 10 kuma za ta gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike.

Leave A Reply

Your email address will not be published.