Sojojin Saman Najeriya ta halaka hatsabibin jagoran masu garkuwa da mutane, Janari, a Kaduna

0
141

Daga Maryam Umar Abdullahi

An kashe wani mai garkuwa da mutane da aka fi sani da Janari tare da tawagarsa a hare-haren da sojojin saman Najeriya suka kai ta sama.

Kakakin hukumar ta Sojojin Sama (NAF), Air Vice Marshall, Edward Gabkwet, ya ce an kashe Janari da maƙarraban sa ne a ranar Alhamis, 18 ga watan Janairu, a wani wuri kusa da Gadar Katako a ƙaramar hukumar Igabi.

Ana zarginsu da kai hare-hare da sace-sace da dama a cikin jihar Kaduna da kuma kan hanyar Abuja zuwa Kaduna. An ba da izinin kai hare-hare ta sama bayan da aka ga Janari da ‘yan ƙungiyarsa a wani wuri kusa da Gadar Katako a ƙaramar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

KU KUMA KARANTA: Wani Soja ya bindige kansa a Abekuta

Sanarwar ta ce; “Bayan bayanan da aka samu sun nuna cewa lallai an kawar da Janari tare da wasu ‘yan ta’adda/ masu garkuwa da mutane da dama.

“An kuma kai irin wannan harin ta sama a ranar 20 ga watan Janairun 2024 akan maɓoyar ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a kusa da Chukuba a jihar Neja tare da samun nasarori daban-daban.

“Bayanai da aka samu bayan hare-haren ya nuna cewa bayan halaka ‘yan ta’addan, an kuma lalata ƙarfinsu na motsi da ababen hawansu.”

Leave a Reply