Gwamnatin tarayya ta amince da sanya hijabi a makarantun sakandare

4
371

Gwamnatin tarayya ta amince da amfani da hijabi ga ɗalibai mata. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar 1ga watan Fabrairu, mai ɗauke da sa hannun babban sakataren ma’aikatar ilimi ta tarayya, Andrew David Adejo.

An aika saƙon ne ga ɗaukacin shugabannin kwalejojin haɗin kan gwamnatin tarayya guda 112 da kuma kwalejojin kimiyya da fasaha na ƙasar! nan.

KU KUMA KARANTA: Ku rubuta ku aje, nan bada jimawa ba kotu zata yi watsi da dokar da ta bawa mata ta sanya Hijabi a Legas – Omirhobo

A cewar sanarwar, “Wannan saƙon ya kawo muku sanarwa cewa ma’aikatar ta amince da amfani da hijabi a matsayin wani ɓangare na kayan makaranta da ɗalibai mata musulmi zasu dinga amfani da shi a dukkan kwalejojin haɗin kan gwamnatin tarayya da na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya.”

Ya yi bayanin cewa ɗaliban makarantun biyu za su iya amfani da hijabi a kan kowace sutura da makaranta ta amincewa.

Sai dai sanarwar ta yi gargaɗin cewa kada tilasta dalibai yin amfani da hijabin ba tare da ra’ayin ta ba.

4 COMMENTS

Leave a Reply