Ku rubuta ku aje, nan bada jimawa ba kotu zata yi watsi da dokar da ta bawa mata ta sanya Hijabi a Legas – Omirhobo

1
285

Daga Fatima Hassan GIMBA, Abuja

Biyo bayan hukuncin da kotun koli ta yanke na tabbatar hakkin dalibai mata musulmai a jihar Legas na sanya Hijabi a makaranta, wani lauya dan Najeriya, Malcolm Omirhobo, ya haifar da cece-kuce ta hanyar sanya tufafin gargajiya a lokacin da ya bayyana a kotu.

A cikin wata hira da jaridar The Cable, lauyan ya yi magana ne kan salon sa tufafin da ba’a saba gani ba, da kuma abin da yake ganin kotun koli zata yi game da hukuncin da aka yanke na Hijabi.

Tambaya: Shin kana adawa da hukuncin da kotun koli ta yanke kan Hijabi saboda kuna yin wani addini daban?

Omirhobo: Ba ina magana ne kawai kan Hijabi ba, gaskiyar magana ita ce muna duban zaman lafiyar Najeriya — cewa dukkan addinai daidai suke kuma babu wani addini a hukumance, don haka bai kamata a fifita addini ba.

Tambaya: Menene zai faru idan kotun ba ta soke hukuncin da ta yanke ba?

Omirhobo: Ku rubuta ku ajiye, zasu canja shi, yanzu muka fara; za mu yi ta bin shari’ar muna da hanyoyi daban-daban, don yanzu daga karar wannan shari’ar zuwa kotun koli. Watakila ba kai tsaye ba, amma za’a sami shawarar da za ta canja wannan.

Akwai wani abu da suke kira ‘Locus standi’ a doka kafin ka kawo kara zuwa kotu, dole ne ka sami isasshen ra’ayoyi. Don haka mafi yawan lokuta musamman ma lokacin da ya shafi maslahar jama’a, idan an kawo za su jefar da shi su ce ba ka da ‘Locus standi’ kuma kai mutum ne kwalli daya kawai.

1 COMMENT

Leave a Reply