Kotu ta bada umarnin a kamo shugaban APC na Kano, Abbas Abdullahi Abbas

0
251

Daga Saleh Inuwa, Kano

An bayar da umarnin tsare shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abbas Abdullahi Abba wanda ake wa laƙabi da ɗan sarki jikan sarki.

Wata babbar kotun tarayya da ke Kano ce ta bayar da umarnin.
Kotun ta ba da umarnin a kama shi domin bincike kan kalaman da ya yi.

Ana zargin jiga-jigan jam’iyyar da barazana ga rayuwa, da kawo cikas ga zaman lafiya da kuma kalaman nuna ƙiyayya a ƙarar da Mahmoud Lamido ya shigar.

KU KUMA KARANTA:NNPP ta bukaci a kama shugaban APC na Kano

Ɗan sandan na Kano mai zaman kansa, ta bakin lauyansa Bashir Yusuf Muhammad, ya shaida wa kotun cewa Abbas, a wata wayar tarho, ya zayyana cewa zai kashe shi (sai na batar da kai).

A cikin takardun bayanai da kafafen yaɗa labarai suka samu, Mai shari’a S. A. Amobeda ta ɗage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 16 ga watan Fabrairu domin sa ido kan yadda ake bin doka.

Jam’iyyar NNPP, a Kano, ta bayyana hukuncin a matsayin wani babban ci gaba ga dimokradiyya.

Mai magana da yawun yaƙin neman zaɓen jam’iyyar, Sanusi Bature ya ce Abbas ya kasance abin tattaunawa wajen jama’a saboda kalamansa da ka iya kawo cikas ga zaman lafiya.

Bature ya yi nuni da cewa, wannan ne karo na biyu da kotu ta umurci kwamishinan ‘yan sanda da ya kama shugaban jam’iyyar APC tare da gurfanar da shi gaban kuliya bisa zargin cin zarafi, barazana da.

“Muna fatan wannan zai zama darasi ga duk wani ɗan siyasa da ya zaɓi hanyar tashin hankali fiye da inganta zaman lafiya a Kano da Najeriya,” in ji shi.

Leave a Reply