NNPP ta bukaci a kama shugaban APC na Kano

2
252

Ɗan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) Alhaji Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida Gida, ya yi kira da a gaggauta kama shugaban jam’iyyar All Progressives Congress na Kano, Abdullahi Abbas tare da gurfanar da shi a gaban kuliya.

Mai magana da yawun Abba Gida Gida, Sanusi Bature Dawakin Tofa, a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Litinin ya zargi shugaban jam’iyyar APC na jihar da tayar da tarzoma da kuma kitsa siyasa. Abba Kabir ya ce shugaban jam’iyyar APC na jihar ya yi ƙaurin suna wajen yin kalaman nuna ƙiyayya da cin zarafi.

Ya ce ya kamata ya kama shin domin a dawo da mutunci a harkokin siyasa. Dangane da zargin kitsa rikicin, Abba Gida ya ce, akwai faifan sauti da bidiyo da dama na shaida wanda za a iya kafa hujja dasu.

Don haka ya yi kira ga jami’an tsaro da su kama shugaban jam’iyyar APC tare da gurfanar da shi gaban kuliya.“Don haka muke jan hankalin hukumomin tsaro, da duk masu ruwa da tsaki ciki har da sauran Jam’iyyun siyasa waɗanda su ma Abdullahi Abbas ke tsoratar da su da su ɗauki matakin da ya dace kan Shugaban APC Abdullahi Abbas da ɗansa Sani Abdullahi Abbas,” in ji wani bangare na sanarwar.

Jam’iyyar NNPP ta kuma jaddada cewa idan ba a magance hakan ba, to ba za a bar su da wani zaɓi da ya wuce neman wata hanyar kare kansu da mambobinsu ba.kuma hakan na iya sa su ƙauracewa rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.

“Muna kuma so mu bayyana a fili cewa idan ba a magance kalaman Abdullahi Abbas na tashe-tashen hankulan siyasa ba, ba za a bar mu da wani zabin da ya wuce mu kaurace wa rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya mai zuwa da kwamitin sulhu na ƙasa zai fara.”

Jagorancin tsohon shugaban ƙasa, janar Abdussalam Abubakar da duk wata yarjejeniya tsakanin jam’iyyu kan zaben 2023, yin hakan ba zai iya ba da tabbacin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar Kano ba,” in ji sanarwar.

2 COMMENTS

Leave a Reply