Zaɓen 2023: Matsayar kafafen yaɗa labarai na Arewa, daga Ɗan Agbese

3
496

Yayin da ‘yan Nijeriya ke shirye-shiryen zaben shugaban ƙasa da na gwamnoni da ‘yan majalisu a zaben 2013 mai zuwa, kafafen yaɗa labarai na Arewacin Najeriya sun ɗauki matsayar bada shawarwari, domin saita alƙiblar masu kaɗa ƙuri’a na yakin, da kuma masu neman madafun iko, a wani ɓangare na irin gudunmuwar da za su iya bayar a zaɓen.

Kwanan ne hukumar ƙididdiga ta ƙasa, ta fitar da mizanin matsanancin talaucin da ake fuskanta a Nijeriya, kuma sakamakon abin Allah-Wadai ne, domin rahoton ya nuna aƙalla ‘yan Nijeriya miliyan 133, kwatankwacin kashi 63 cikin 100 duk matalauta ne, kuma mutane miliyan 86, kwatankwacin kashi 65 cikin 100 ‘yan Arewa ne.

Don haka ba abin mamaki ba ne, idan aka kwatanta yankin Arewa, wanda shi ke da rinjayen yawan al’umma, a matsayin yanki mafi haɗarin zama a faɗin kasar nan.

Don haka ya zama wajibi, duk masu hanƙoron neman shugabanci a zaɓen shekara ta 2023, su fito fili, su bayyana shirin da su ke da shi na ceto waɗannan tarin mutanen da ke fama da ƙuncin rayuwa, mutanen da rashi ya yi wa ƙatutu, musamman ta fuskar kiwon lafiya, da rashin isasshen abinci da kuma muhalli.

Wannan fa kari ne ga adadin matalautan da ke zaune a yankunan karkara, inda mazauna yankin ke da kashi 72 cikin 100, akasin kashi 42 na wadanda ke zaune a cikin birane.
Daya daga cikin musabbabin ta’azzarar matsanancin talauci musannan a yankin arewa, shi ke ta’azzarar matsalar rashin tsaro.

Daga matsalar Boko Haram, da rikicin manoma da makiyaya, sai kuma ayyukan ta’addancin ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane. Kiri-kiri, yanki ya zama tamkar mayanka.

Sai dai ba abin mamaki ba ne, kasancewar talauci ya janyo matasan da ba su da aikin yi ana ɗauka su aiki a matsayin ‘yan daba, ko kuma ‘yan ta’adda zaune tsaye.
Mu fara da yankin Arewa maso Gabas, inda ta’addancin Boko Haram ya mamaye, duk da dai dakarun sojin Nijeriya sun ci galabar mayakan a wasu yankunan, zuwa yankin tsakiyar Nijeriya, inda rikicin manoma da makiyaya ya yi wa dabaibayi, da kuma yankin arewa maso Yamma, inda ‘yan bindiga su ke cin karen su babu babbaka, ana ji ana gani, ana ta zubar da jinin mutane tsawon shekaru 15 a yankin Arewa, tun bayan kisan da ‘yan sanda su ka yi wa shugaban ‘yan Boko Haram Muhammad Yusuf.

Haka nan dai rashin tsaro ya yi ta ta’azzara har zuwa shekara ta 2015, wanda shi ne musabbabin zaɓen gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Sai dai abin bakin cikin shi ne, tsawon shekaru bakwai ayyukan ta’addanci sai ma abin da ya yi gaba, lamarin ma sai ya zo da dalailai daban-daban.

Tuni dai rahotanni sun bayyana cewa, a jihohin Zamfara da Sokoto, ‘yan bindiga ke tsara wa ‘yan siyasa wuraren da za su gudanar da gangamin yakin neman zabe, da kuma lokacin da za su yi, wannan ba ƙaramin haɗari ba ne, kuma idan har wannan baƙin lamarin ya cigaba a haka, ina mai tabbatar maku cewa babu ranar ƙarewar ayyukan ‘yan bindiga, musamman a ce wai su ke ba ‘yan siyasa kariya.

Lamarin nan fa ba abin lamunta ba ne jama’a, duk wanda ya san ya isa, kuma ya na neman mukamin siyasa, dole ya ƙ hoiudiri kawo karshen ayyukan ‘yan bindiga, ba wai ya kulla alaka da su ba.
Ayyukan ta’addaci dai sun tagayyara al’umma, kuma kalaman yadda za a kawo karshen lamarin ne kawai zai iya sama wa masu neman mukaman siyasa kuri’un masu zabe.
Muna kuma gargadin masu kada ƙuri’a su yi taka-tsatsan da duk wasu ‘yan siyasar da aka san su na hulda da ‘yan bindiga.

Wani bangare na matsalolin da rashin tsaro ya haifar kuma shi ne, ilimin yara ya shiga halin ni-‘yasu, domin a yankin Arewa, ilimin yara ya faɗa cikin mawuyacin hali.
Daga fashin jirgin ƙasa, kiri-kiri an kassara bangaren ilimi. Misali, a shekara ta 2020, ɗalibai 300 aka sace a Kwalejin Kimiyya da ke Kankara a jihar Katsina, sannan a cikin watan Mayu na shekara ta 2021, ɗaliban Islamiyya 130 aka sace daga wata makarantar Islamiyya ta Salihu Tanko da ke garin Tegina a jihar neja.

Sannan duk a cikin watan Mayu na shekara ta 2021, an sace dalibai 126 daga wata makarantar kiristoci ta Bethel Baptist da ke Damishi a jihar Kaduna, yayin da a cikin watan Yuni na shekara ta 2021, aka sace dalibai mata 112 daga Sakandaren Gwamnatin tarayya da ke Yauri a jihar Kebbi, baya ga daliban jami’ar Greenfield da aka sace a jihar Kaduna, da sauran matsaloli makamanta wannan ga su nan ba iyaka.

Wasu daga cikin ‘yan matan da aka sace ma tuni sun haifa wa ‘yan bindiga ‘ya’ya a cikin dazuzzuka, kuma an bar iyaye su san yadda su ka yi da ilimin ‘ya’yan su mata. Wannan fa ya na daga cikin musabbabin ta’azzarar adadin yaran da ba su zuwa makaranta.

Duk wani mai neman madafun iko ba sai an yi nisa ba, domin duk kalubalen da ake fuskanta an san su, don haka duk wani matakin riga-ƙafi ba abu ne mai wahala ba, ‘yan Nijeriya maganin matsalolin da su ke addabarsu su ke buƙata a yanzu.

Yankin Arewa dai bai tsaya a kan matsalar ‘yan bindiga kawai ba, ya zama dandalin miliyoyin ‘yan gudun hijirar da ‘yan ta’adda su ka tagayyara, sun rasa muhallan su, rayuwar su ta shiga garari, don haka akwai buƙatar ɗaukar matakin gaggawa, domin a maida su garuruwa da muhallan su na asali.

Babu wani dan siyasar da zai zo gobe ya ce bai san yadda wannan bala’in ya riski mutane ba, don haka ba su da wata hujjar neman shugabanci, matuƙar ba su da shirin kawo karshen manyan kalubalen da jama’a ke fuskanta.

Kafafen yaɗa labarai na yankin arewa sun yi gargadin yiwuwar haramta ma wannan tarin bayin Allan ‘yan cin jefa ƙuri’un su, don haka su ka ja hankalin hukumomin tsaro su tabbatar sun ba ‘yan gudun hijira kariya, hukumar zaɓe kuma ta shirya yadda za a ba su damar jefa ƙuri’a domin zaɓen wanda su ke so ya shugabance su.

Kafafen yaɗa labaran, sun kuma yi Allah-Wadai da salon gangamin yaƙin neman zaɓen da ake yi a Nijeriya, inda ‘yan siyasa ke cin zarafin abokan hamayya maimakon maida hankali a kan abin da zai amfani al’umma.

‘Yan siyasa sun gwammace amfani da kalaman cin zarafi, su na amfani da addini, maimakon su maida hankali a kan matsalolin da al’umma ke fuskanta,
ɓangaren ilimi dai ya shiga tasku, inda har yanzu rikici tsakanin kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU da gwamnatin tarayya bai ƙare ba.

Aikin yi ya gagari miliyoyin ɗaliban da suka kammala jami’a a Nijeriya.
Akwai bukatar a samar da shirye-shiryen yadda za a farfado da tattalin arzikin mu, a samar da ayyukan yi ga aƙalla matasa miliyan 30 da ke zaman kashe wando.
Ba mu bukatar masu ɓaɓatun fatar baki ko wadanda ba su ɗauki rayuwar jama’a da mahimmanci ba, muna bukatar ƙwararan shirye-shirye gabanin zaɓen shekarar 2023.

Babu abin da yankin arewa ke buƙata a daidai wannan lokacin, illa ƙwaƙƙwaran shirin kawo karshen matsanancin talauci da yunwa da takaicin da al’ummomin yankin ke ciki.

Don haka muna bukatar a inganta yankin Arewa da ma Najeriya baki ɗaya kowa ya samu yalwa.

‘Yan Nijeriya dai su na sa ran a gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe a shekarar 2023.

Wani abin burgewa shi ne, dokar zabe ta shekara ta 2022, ta samar da Na’urar tantace masu kaɗa kuri’a ta BVAS, inda za a rika tura sakamakon zaɓe kai tsaye ta yanar gizo.

Ga dukkan alamu dai, da kuma rawar da hukumar zabe ta taka a zabubbukan jihohin Anambra da Ekiti da Osun, amfani da wadannan na’urorin ya tabbatar da cewa zai yi wahala a iya yin maguɗin zaɓe, lamarin da ya ba ‘yan Nijeriya ƙwarin giwar cewa ba za su yi asarar kuri’un su ba.

Muna kuma jan hankalin masu kaɗa ƙuri’a, su yi amfani da wannan dama da hukumar zaɓe ta samar, wajen amfani da na’u’rorin zamani yayin gudanar da zaɓe, ta yadda nan gaba hatta siyasar kuɗi za ta zama tarihi a Nijeriya.

Wannan, matsayar ƙungiyar kafafen yada labarai ta Arewacin Najeriya Kenan, ɗauke da sa hannun shugaban ta Dan Agbese, da sakatariyar ƙungiyar Zainab Suleiman Okino.

3 COMMENTS

Leave a Reply