Adam A Zango, jarumin mu na wannan makon

Adam A Zango ɗan wasan kwaikwayo ne na Najeriya, mawaƙi, darakta, furodusa, marubucin, kuma ɗan agaji. An haife shi a watan Oktoba, 1985, a Zangon Kataf a jihar Kaduna. Kimanin dukiyarsa ta kai kimanin Naira miliyan 300.

Adam Zango, wanda aka fi sani da yariman Kannywood, na ɗaya daga cikin masu faɗa a ji a Kannywood. Ya samu karɓuwa gurin mutane dayawa, musamman mata saboda yanada kyau na halitta, da kuma iya wanka. Mutanen da suka sanshi da wanda ma basu sanshi ba sun sheda irin kyautar sa, da yadda baya qyashin raba dukiyar sa, a duk inda ya tsinci kansa. Ko a harkar wajen aiki da biyan ma’aikata, Adamu an sheda hannunsa a buɗe yake, baya ƙaramar harka.

Ya fara sana’ar sa tun a shekarar 2001 yana ɗan shekara 16. Ya fara da harkar waƙa ne, ya kuma kai matsayin fitaccen jarumin fina-finan Hausa a cikin ƙanƙanin lokaci saboda hazaƙarsa da ƙwazonsa.

Adam Zango yana da waƙoƙi da dama da suka yi fice kuma ya shahara a Najeriya da sauran ƙasashen waje. A shekarar 2014, ya samu lambar yabo ta gwarzon ɗan wasa a kyautar fina-finan Afirka. Ya kuma lashe kyautar gwarzon mawakin Kannywood na hip-hop, da kuma fitaccen jarumin Kannywood a kyautar fina-finan mutanen birni a shekarar 2015.

Adamu, a lokacin da yai bikin zagayowar ranar aurensa na shekara 3

Wasu daga cikin waƙoƙinsa sun haɗa da Soyayya, Aure, Gambara, da dai sauransu. Ya fito a fina-finai sama da 200, da suka haɗa da Basaja, Hindu, Bayan Rai, Shaheeda, da wasu silsila. Ya fito kuma a shirye-shiryen Farin Wata sha Kallo da Asin da Asin a YouTube.

Ganin cewa Kannywood na biyansa Average na 200k -500k a kowane fim, ya danganta da irin rawar da Adam Zango ya taka a fim ɗin, za a iya cewa wani muhimmin ɓangare na arziƙin Adam Zango ya fito ne daga fina-finan.

KU KUMA KARANTA: Saratu Zazzau ‘Dr Girema’ ta kwana Chasa’in ta amarce

Baya ga kasancewar Adam A Zango ɗaya daga cikin jaruman fina-finan da suka yi nasara, Adam A Zango yana ɗaya daga cikin manyan jaruman Kannywood da suka fi kowa kuɗi, tare da sauran jarumai kamar Ali Nuhu, Nazir Sarkin Waƙa, Rahama Sadau, da sauransu.


Comments

4 responses to “Adam A Zango, jarumin mu na wannan makon”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Adam A Zango, jarumin mu na wannan makon […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: Adam A Zango, jarumin mu na wannan makon […]

  3. […] KU KUMA KARANTA: Adam A Zango, jarumin mu na wannan makon […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *