Alamara: Tururuwa ta cinye takardun shaidar kashe kuɗaɗe a asusun inshoran NSITF

0
463

Daga Fatima GIMBA, Abuja

wani bincike da ake yi ya tono garma a asusun inshora na NSITF, masu gudunarwa sun yi tsokaci game da binciken Asusun ya shaidawa majalisar dattawa cewa, akwai yiwuwar ruwan sama da tururuwa sun cinye wasu takardu masu muhimmanci Ba wannan ne karon farko da hukumomi a Najeriya ke ta’allaka wata badakala da aukuwar bala’i daga dabbobi ba.

FCT, Abuja – Asusun inshora na Najeriya na NSITF ya shaida wa Majalisar Dattawa cewa tururuwa ta cinye mafi yawan takardun da ke dauke da cikakkun bayanai na yadda aka sarrafa N17.158bn da har yanzu ba a tantance ba. Kudaden, kamar yadda ya bayyana a rahoton tantancewa na 2018, N17.58bn ne jimillar da NSITF ta tura daga asusun bankinta na Skye Bank da First Bank zuwa wasu asusu daban-daban na mutane da kamfanoni da ba a iya gano tushensu ba daga watan Janairu zuwa Disamba 2013.

Ofishin babban mai binciken kudi a rahoton binciken na 2018 ya gabatar da korafe-korafe guda 50 da suka danganci karkatar da kudaden da hukumar gudanarwar NSITF ta yi, wanda kwamitin majalisar dattijai mai kula da asusun gwamnati ke bincikensa.

Game da kashe N17.158bn da NSITF tayi ba tare da wata hujja ba, tambayar ta karanta kamar yadda Leadership ta ruwaito: DUBA: Shigo shafin na manhajar na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka “Gudanarwar NSITF kamar yadda aka gani a bayanan lambar asusu 1750011691 na Skye bank plc, daga 1 ga Janairu, 2013 zuwa 20 ga Disamba, 2013, da kuma bayanan asusun mai lamba 2001754610 na First Bank Plc daga 7 ga Janairu, 2013 a ranar 28 ga Fabrairu, 2013, ta tura kudaden da suka kai N17,158,883,034.69 ga wasu mutane da kamfanoni daga wadannan asusun.”

Ya ce: “Ma’ajiyar da aka ce takardun da jami’an da suka gabata suka ajiye, ba wai ruwan sama ne kadai ya buge su ba a tsawon shekaru, ta yiwu ma tururuwa ta ne cinye su. “Kamar yadda wannan kwamiti ya ba da umarni, na shaida wa jami’an gudanarwar da suka gabata bukatar su taimaka mana wajen amsa wannan tambaya tare da kawo muhimman takardu da ba a ba mu ba.”

Sai dai a nasa jawabin, Manajan Daraktan NSITF daga 2010 zuwa 2016, Umar Munir Abubakar, ya ce bai da masaniya kan wannan batu, kuma ba shi da wani bayani a kai tunda ba a gudanar da tantancewar a zamaninsa ba, rahoton Daily Sun. Magajinsa, Mista Adebayo Somefun wanda ya rike mukamin daga Mayun 2017 zuwa Yuli 2020, ta’allaka laifin batar takardun ga manajan daraktan na yanzu. Cikin fushi da bayanan NSITF, kwamitin ya umarce su da su sake gurfana gaban kwamitin tare da dukkan takardun shaida da aka nema ba tare da kawo wani uzuri ba a ranar Alhamis, 22 ga Satumba, 2022.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here