Matashi mai shekaru 16 ya rataye kansa a jihar Kano

0
305

Daga Shafa’atu DAUDA, Kano

Wani matashi mai kimanin shekaru goma shashida mai suna Ibrahim Lawan ya rataye kansa a ƙauyen Kuki dake karamar hukumar Bebeji a jihar Kano dake ƙarƙashin ikon masarautar Rano.

Jami’in yaɗa labarai na masarautar Nasiru Habu Faragai shine ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aikewa manema labarai.

Sanarwar ta baiyana cewa Hakimin Bebeji Maji Daɗin Rano, Alhaji Tijjani Abdullahi Kuki, ya gabatarwa mai Martaba Sarkin Rano, Ambassador kabiru Muhammad Inuwa rahoton faruwar lamarin, Wanda ya faru a ranar 14 ga watan Agustan da muke ciki, inda aka tarar da matashin tuni rai ya yi halinsa.

Inda Sarkin Rano ya buƙaci a mika rahoton ga jami’an ‘Yan sanda domin fadaɗa bincike.

Da yake karɓar rahoton, Sarkin ya buƙaci Hakimai da Dagatai da masu Unguwanni dake masarautar da su tashi tsaye wajen gudanar da addu’oi domin neman ɗauki Allah daga samun faruwar irin wadannan matsaloli.

Jaridar Neptune prime ta tuntuɓi rundunar Yan sandan jihar ta bakin kakakinta Abdullahi Haruna Kiyawa, sai dai bai sami amsa kiran da mukai masa ba.

Leave a Reply