Mace ta farko da ta auri kanta, a Indiya

0
303

Wata ’yar Indiya mai suna Bindu ta kafa tarihin zama mace ta farko da ta auri kanta da kanta a ƙasar Indiya, wanda biki ya jawo ce-ce-ku-ce.

Bindu, mai shekara 24 da haihuwa daga yankin Gujurat na ƙasar ta ce ta samu dabarar yin hakan ne daga wani shirin talbijin na Netflix da ake nunawa a ƙasar.

Bayan ta gamsu da cewa auren kanta da kanta shi ne ya fi dacewa da ita, Bindu ta nemi da ta ɗaura auren a wajen bautarsu na Hindu amma duk wuraren bautar suka ƙi yarda.

Bindu, A yayin shagalin bikin ta

Wani malamin abin bautarsu na addinin Hindu wanda da farko ya amince ya daura auren, shi ma bayan an sa rana, sai janye saboda la’anta da kuma kyamatar abin da Bindu ke shirin fuskanta daga jama’ar gari.

Da ranar ta zo, Bindu ta sha kwalliya irin ta amare tare da yin lalle, inda ta ɗaura auren a gidanta a wani ɗan ƙwarya-ƙwaryar biki da rawa da ’yar ƙwarya-ƙwaryar walima da addu’oi na addinin Hindu, a ƙaramar lasifikar rediyo.

Wannan abin da Bindu ta yi ya janyo ce-ce-ku-ce da kuma daukar hankalin jama’a a kafafen sada zumunta da kuma kafafen yaɗa labaran ƙasar.

Wani mai fada a ji a jam’iyyar BJP mai mulkin ƙasar, mai suna Sunita Shukla ya ƙalubalanci al’amarin tun kafin a yi, domin kuwa sai da ya gargaɗi malaman addininsu da kuma wuraren bautarsu da kada su kuskura su ɗaura auren Bindu da kan nata.

Ya shaida wa ’yan jarida cewa, “Ba za mu bari a yi wannan aure ba a kowane wurin bauta na Hindu, soboda haramtacce ne kuma hakan zai iya rage mabiya wannan addini.”

Bindu dai na ci gaba da fuskantar ƙyama, baya ga fuskantar wariya daga ’yan uwa da makwabta bisa abin da ta aikata din.

Sai dai da alama ita ko a jikinta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here