Dalilin da ya sa matashi ya hau allon tallace-tallace a Kano

0
66
Dalilin da ya sa matashi ya hau allon tallace-tallace a Kano

Dalilin da ya sa matashi ya hau allon tallace-tallace a Kano

Daga Shafaatu Dauda Kano

Wani Matashi ɗan kimanin shekara 27 ya hau allon tallace-tallace da ke kusa da Gadar Lado a Kano, inda ake zargin yana shirin tsalle ya fado kasa.

Wannan lamari ya haddasa cinkoson Ababen Hawa a hanya, yayin da jama’a suka taru suna kallon abin da ke faruwa.

Wasu daga cikin al’umma sun bayyana cewa matashin ya shafe mako guda yana neman haduwa da wani mashahurin ɗan Tiktok a Kano dake titin zuwa gidan namun daji, amma hakan bai yiwu ba.

KU KUMA KARANTA: Ana Zargin wani magidanci da kashe ‘yarsa Sakamakon Dukanta da Itace a kano

Sai kawai aka hangoshi yana zaune a sama akan allon tallace-tallace.

Mutane sun yi curko-curko a bakin gadar, inda suka rika furta albarkacin bakinsu.
A yayin da wasu ke kiransa ya fado, wasu kuma na roƙon Allah ya shiryar da shi.

Domin samun haske game da wannan al’amari, Wakiliyar Neptune prime ta tuntubi wani malamin addinin Musulunci mai suna Malam Dabarani Bin Sa’id.
Ya bayyana cewa cikar imani ga bawa shine yadda da kaddara, mai kyau ko mara kyau, tare da dogaro da Allah.

Leave a Reply