Sanata Abdullahi Adamu Ya Zama Sabon Shugaban Jam’iyyar APC Mai Mulki A Najeriya

0
432

Daga; USMAN NASIDI.

AN bayyana tsohon Gwamnan Jihar Nasara, Sanata Abdullahi Adamu a matsayin wanda ya yi nasarar zama sabon Shugaban Jam’iyyar APC ta Kasa a yayin gangamin taron Jam’iyyar ta APC daya gudana a garin Abuja.

Gwamnan Jihar Jigawa Muhammadu Badaru ne ya sanar da hakan a yayin babban taron Jam’iyyar bayan duka waɗanda suke takarar sun janye wa Abdullahi Adamu.

Kafin sanar da shi a matsayin sabon shugaban, sai da Gwamna Badaru ya tambayi wakilan zaɓe ko kuma deliget kan cewa sun amince da Abdullahi Adamu a matsayin sabon shugaban APC, sai suka ce sun amince.

Tun kafin a soma taron dama ana ta raɗe-raɗin cewa za a samu maslaha a ba Abdullahi Adamu shugabancin, inda a yayin taron ne masu takarar suka sanar da cewa duk sun janye.

Bayan dawowar demokradiyya a 1999, Abdullahi Adamu ya zama gwamnan Jihar Nasarawa bayan samun nasara a zabe, kana bayan karewar wa’adinsa na farko, ya sake takara a 2003 kuma ya yi nasara.

Bayan sauka daga gwamna a 2007 da hutun shekaru hudu, Abdullahi Adamu ya koma majalisar dokokin tarayya wakiltar mazabar Nasarawa ta yamma a majalisar dattawa a 2011.

Akalla, shekaru 44 na rayuwarsa a siyasar Demokoradiyya amma bai taba fadi zabe ba, wanda wannan wata babban nasara ce da Sanata Abdullahi Adamu kuma ya ke alfahari da ita domin tun da ya shiga siyasa ba’a taba kada shi ba tun 1978.

Hakazalika a kwanakin baya ya ce: ” tun daga 1978 zuwa yanzu, ban taba fadi wani zabe ba. Ni ne kusan mutumin karshe da ya bayyana niyyar takara da gangan nayi hakan.”

Leave a Reply