Duk Abin Da Yake Mai Kyau Da Zai Amfani Yan Najeriya Buhari Zai Sa Hannu – Sanata Gobir

0
289

Daga; Bashir Bello, Majalisa Abuja.

SANATA Ibrahim Abdullahi Gobir, mai wakiltar Jihar Sokoto ta gabas a Majalisar Dattawa, ya bayyana cewa duk abu mai kyau da yan najeriya za su iya amfana dashi shugaban kasa Muhammadu Buhari zai aminta da sa hannu.

Ya kara da cewa wannan kudirin da ya kawo kana ya gabatar domin Sarrafa makamashi da ake da su a kasar, wani abu ne wanda zai amfani yan Kasar baki daya, sannan da tabbatar da an samu ci gaba ta fannin raya kasar Najeriya da al’ummar ta da abubuwan more rayuwa.

Ya ce “kowani irin makamashi muke amfani da shi yana cikin wannan kudirin domin babu wani abu wanda baya ciki. Kun ga idan muna maganar Gawayi, Man Iskar Gas, Man Fetur, Wutan Lantarki, Wutar Hasken Rana, Danyen Mai da duk wasu abubuwan da ake tsammani ta fannin Wutan Lantarki ba za a samu matsala ba.”

“Amma yanzu ace kamar Najeriya, wuta ma babu, kuma ba bu makamashi a nigeriya, toh kun ga ko akwai matsala, duk da cewa dama akwai wata cibiya ta wuta wacce ita ce ya kamata ta rika zakulo duk irin wadannan abubuwan A sarrafa su.”

A cewarsa, kirkirar wasu abubuwan da za a rika amfani da su domin sarrafa sinadarin Carbon Monoxide wani abu ne wanda zai taimaka wa fannin samar da abubuwan da ake bukata a cikin kasar wadanda al’umma za su samu ci gaba ta fannin samun saukin gudanar da rayuwa.

A karshe, Sanata Ibrahim Gobir, ya bayyana cewa Allah Ya albarkace mu da duk wasu abubuwan da muke bukata domin samun Ingantaccen rayuwa, Shugaba Buhari zai saka hannu a kudirin muddun idan zai am fani al’ummar Kasar baki daya.

Leave a Reply