Bello Turji Babu Sauran Turjiya Sulhu Yake Nema

0
515

Rahotanni daga jihar Zamfara a Najeriya na cewa ƙasurgumin ɗan fashin dajin nan da aka fi sani da suna Bello Turji ya saki wasu gomman mutane da suka daɗe suna tsare a hannunsa.

Riƙaƙƙen ɗan fashin, na cikin manyan jagororin ‘yan fashin dajin da suka fi ƙaurin suna wajen kashe-kashe da satar mutane don neman kuɗin fansa musamman a tsakanin jihohin Zamfara da Sokoto.

Jaridar Daily Trust ta ambato wasu majiyoyi da ke cewa a watan jiya, Bello Turji ya rubuta wa Masarautar Shinkafi wasiƙa inda yake jaddada aniyarsa ta hawa teburin tattaunawa da nufin ajiye makamansa da kuma rungumar zaman lafiya.

A cewarta, sakin gomman mutanen, wani ɓangare ne na tattaunawar da ake yi da Turji.

BBC ta ji ta bakin wani wanda ya ga wasu daga cikin wadanda aka sako daga dajin.

“Da misalin ƙarfe biyar na maraice zuwa shida, shi Bello Turji ya sako waɗannan mutane, kuma aka je aka zo da su zuwa Area Command na rundunar ‘yan sanda da ke nan cikin garin Shinkafi.

Ya ce ba da jimawa ba kuma aka wuce da su zuwa Gusau babban birnin jihar Zamfara.

Ya kara da cewa “wasu cikin ‘yan uwan wadanda aka sakon sun gana da su har ana ta murna.”

Da aka tambaye wannan shaidan ko a me aka kwaso wadanda aka sakin, sai ya ce: “An kawo su ne a motoci. Bakin gulbi Bello Turji ya ajiye su a kusa da wani ƙauye da ake ce ma Mabera da bai wuce kilomita uku ko hudu ba daga garin Shinkafi.”

An kuma tambaye shi ko mutum nawa aka sako, inda ya ce, “Gaskiya duka ya sako, amma ba zan iya tantance yawansu ba saboda suna da yawa sosai.”

Ya ce akwai wadanda suka ce wadanda aka sakon sun kai mutum dari, amma shi dai bai iya ƙirga su ba.

Wannan shaidan ya bayyana cewa Bello Turji ya sako dukkan wadanda ya ke garkuwa da su ne saboda yana neman hanyar sasantawa da hukuma ne.

“Yana neman yaga ya daidaita lamurra ne domin a zauna lafiya. Dukkansu ya sako.”

Ya ce cikin wadanda aka sako, akwai maza da mata har ma da ƙananan yara.

“Wasu cikinsu ma suna ɗauke da raunuka, domin lokacin da aka tare su bisa hanya, barayin dajin sun bude musu wuta kuma wasu an harbe su sai dai harbin ba mai matsala ba ne, kuma a haka suka tafi da su daji suka tsare su.”

Ya kuma kara bayyana halin da ya gansu: “Idan ka dube su za ka ga kamar an haƙo su daga cikin kasa ne saboda halin da suke ciki na rashin wanka da rashin wanki, kuma ga ƙura suna zauna a fili cikin daji.”

Kamar yadda ya bayyana, wasu cikin dangin wadanda aka sakon sun yi ta murna bayan da suka sa ‘yan uwan nasu a ido.

“An yi ta raha har zuwa lokacin da aka wuce da su zuwa Gusau.”

Da aka tambayi wannan ganau ɗin ko su wane ne suka karɓo su, sai ya ce, “Lallai mun sami labari cewa shi Bello Turji ne ya nemi hukuma ta je ta karbo su. Zai sako su ba tare da an biya ko sisin kwabo ba.”

Ya ce da alamu hukumar ‘yan sanda ne suka karɓo su daga hannun mutanen Bello Turjin ciki har da ƙananan yara waɗanda shekarunsu na haihuwa ba su wuce bakwai ko takwas ba.

BBC ta nemi jin ba bakin gwamnatin jihar Zamfara amma har zuwa lokacin da muka wallafa wannan rahoton, Kwamishinan Yada Labarai na jihar Ibrahim Dosara bai amsa kiraye-kirayen da muka yi ma sa ba duk da cewa da farko ya amince ya yi ƙarin bayani.

Leave a Reply